Ina Fatan Samun Nasara A Kan Tottenham A Gobe – Solkjaer

Daga Abba Ibrahim Wada

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa yana fatan ‘yan wasansa zasu dage domin doke kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a wasan da za su fafata a gobe Lahadi.
Manchester United dai ta dauki hanyar kai wa wasan daf dana karshe a gasar cin kofin Euopa League, bayan da ta je ta doke kungiyar kwallon kafa ta Granada da ci 2-0 a daren ranar Alhamis.
dan wasa Marcus Rashford ne ya fara ci wa Manchester United kwallo, bayan da dan wasa bictor Lindelof ya buga masa wata kwallo, sannan shi kuma ya buga ta wuce mai tsaron ragar kungiyar, Rui Silba.
dan wasa Yangel Herrera mai buga wasannin aro daga Manchester City ya kai wa Manchester United hari daga wajen da’ira ta 18, amma kwallon ta bugi turken raga sannan kuma mai tsaron raga De Gea ya a mata hannu.
Shima tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Roberto Soldado ya samu wata dama mai kyau, amma da ya buga kwallon sai ta yi fadi ta fita waje duk da cewa ya hadu da dan wasa Harry Maguire kuma sun fafata.
Manchester United ta ci kwallo ta biyu a bugun fenareti ta hannun dan wasanta na tsakiya, Bruno Fernandes, bayan da dan wasa Yan Brice ya yi wa dan kwallon Portugal din keta a da’ira ta 16.
Har ila yau Manchester United wadda za ta karbi bakuncin wasa na biyu a filin wasa na Old Trafford ranar Alhamis, kuma duk wadda ta kai wasan daf da karshe za ta kece raini tsakanin Ajad ko kuma Roma.
kungiyar wadda take ta biyu a kan teburin gasar firimiya ta yi rashin nasara a wasa daya daga wasanni 17 da ta yi a dukkan karawa, za kuma ta ziyarci kungiyar Tottenham a gasar Premier ranar Lahadi.

Exit mobile version