Dan wasan Najeriya Kelechi Iheanacho wanda ya taimaka wa kungiyaar kwallon kafa ta Leicester City samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin FA bayan ya ci mata kwallaye biyu a fafatawar da ta doke Manchester United da ci 3-1 ya bayyana cewa zai ci gaba da nuna bajinta har a wasannin da zai wakilci Nigeriya.
Iheanacho ya jefa kwallon biyu a mintina na 24 da 78, sannan kuma ya taimaka wa Youri Tielemans jefa wata kwallon a minti na 52 hakan yasa jumullar kwallaye tara kenan da dan wasan na Najeriya ya jefa a raga a wasanni tara da ya buga kuma ko a makon da ya gabata sai da ya zura kwallaye uku a ragar Sheffield United.
“Inaa fatan ci gaba da nuna hazaka a wasannin d azan wakilci Nigeriya saboda haka dole ne ragowar ‘yan wasa su bayar da hadin kai domin tabbatar da ganin mun samu irin sakamakon da muke bukata” in ji Iheanacho
A karon farko kenan tun shekarar 1982, wato shekaru 39 da Leicester City ke samun gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin FA kuma yanzu haka Leicester City za ta hadu da Southampton a wasan na dab da na karshe a filin wasa na Wembley a cikin watan Afrilu mai zuwa, inda ita ma Chelsea za ta hadu da Manchester City.