Ina Gode Wa Magoya Bayana A Duniya – Eriksen

Eriksen

Dan wasan tawagar kasar Denmark, Christian Eriksen , ya godwa magiya bayansa da ‘yan uwansa ‘yan wasan kwallon kafa na kasar da kuma duk wanda ya bayar da wata gudunmawa wajen ganin ya farfado daga dogon suman da yayi a ranar Asabar.

Tuni daman hukumar kula da kwallon kafa ta Denmark ta ce dan wasan nata Christian Eriksen ya farfado bayan ya sume a fili kuma yana ci gaba da samun kulawar likitoci kamar yadda aka saba.

Dan wasa Eriksen dai ya fadi ana tsakiyar wasa a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 kuma ya faɗdi ne shi kadai ba kwallo tare da shi a ya yin da ƙkasarsa Denmark ke tsakiyar fafatawa da tawagar ‘yan wasan kasar Finland a ranar Asabar.

Sanarwar da hukumar kwallon kafar Denmark ta fitar ta ce Christian Eriksen ya farfado kuma yana samun sauki amma har yanzu yana kwance a asibiti domin ci gaba da karbar magani daga wajen likitoci.

Amma an kwashi dan wasan a sume a filin wasa, al’amarin da ya sa aka dakatar da buga wasan kuma  abokan wasansa dukkaninsu sun fice daga filin  suna kwalla, wasunsu kuma suna ta addu’a.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai Uefa ta ce an ci gaba da wasan ne bayan tattauna wa da hukumomin Denmark da Finland kuma hukumar ta bayyana cewa tana fatan  dan wasan zai murmure ya ci gaba da buga kwallo nan bada jimawa ba.

Exit mobile version