Alhaji Usman Adamu wanda ake yiwa laƙabi da Doya 50, kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Nasarawa, kuma mazaunin garin Agyaragu, Ɗan siyasa ne da aka daɗe a na damawa dashi a siyasar Jihar Nasarawa. Ya kasance Ɗan a-mutu ko ɗan gani-kashenin gwamna Umar Tanko Al-makura da Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu Zubairu T.M.Lawal a garin Lafia. Ga yadda hirar ta kasance:
Jama’a za su so jin cikakken sunanka?
Sunanan Usman Adamu wanda ake kira doya 50.
Idan ba don lokaci zai yi mana ƙaranci ba, da sai na ce maka ayyukan gwamna Umar Tanko Al-makura idan za mu ƙirga su ɗaya bayan ɗaya, wuri kaza, wuri kaza, to zamu iya kai wa bayan azahar bamu gama ba. Batun cewa Al-makura yayi aiki a Jihar Nasarawa sai dai a riƙa maimaitawa kamar yadda kullum idan mutum ya tashi daga barci da safe sai ya wanke baki. kuma Yaran da ma ba a haife su ba waɗanda za a haifa nan gaba sai sun girma sun yi karatu za su zo su yi tambaya waye yayi wannan aiki, sai a ce dasu Tanko Al-makura ne, a lokacin yana Gwamna. Saboda sunan da ya bai wa kanshi kamar wahayi ne (Gani ya kori ji). Duk inda kake a Nasarawa tun daga Toto har zuwa Tunga babu inda ayyukanshi basu shigaba. Ba cikin biranai kawai ba har Karkara sun ga aiki a ƙasa.
Zuwan Gwamna Al-makura ya buɗewa al’umman Jihar ido ta wajen yin aiki, duk da cewa ya ragewa wasu ‘yan kaɗan jin daɗi, masu wawure haƙƙin al’umma suna zuba wa a aljihu. Idan aka ce me yasa ba a yi aiki ba su ce, babu kuɗi.
Al’ummar Jihar Nasarawa sun amfana da mulkin Tanko Almakura kuma ko maƙiyinsa ne dole ya ce, wannan bawan Allah yayi aiki na a zo a gani. Sai dai kawai idan zai yi ƙiyayya ta wani abu ba ta ɓangaren aiki ba.
Ma’aikata na koka wa cewa ba a biyansu isasshen albashi da kuma rashin biya akan lokaci ko me za ka ce?
Duk da cewa mun daɗe muna magana akan batun ma’aikata, amma zan yi wani magana su saurareni da kunnen basira. Na gode da cewa a Jaridan LEADERSHIP A Yau za a sanya ba a Rediyo ba, ka da ma wani ya ce, bai ji ba, idan a jarida ne sai muce je ka waje kaza, za ka samu jaridan ka saya. Ba yau muke faɗi ba, haƙuri babban abu ne. Akwai lokacin da aka yi yajin aiki a a baya mun yi magana, cewa a bi a hankali ko da ana harbi da bindiga ne a na dawowa tebur a zauna a sasanta.
Na kuma godewa ma’aikatan Jihar Nasarawa waɗanda mu ka ce su yi haƙuri kuma suka yi, to a yau na ji wani labari a majiya mai tushe ya jadada min wai cewa yanzu batun biyan rabin albashi ga ma’aikatan ƙananan hukumomi ya zo ƙarshe, inji kwamishina. Don haka muna fatan duk ma’aikatan jihar Nasarawa, Allah ya sa ƙarshen matsalar biyan albashi ta zo ƙarshe.
Na san cewa ba duka ma’aikata ne suka kasa fahimtar inda a ka sa a gaba ba, akwai waɗanda suke yi domin su ga gazawar gwamnati. To Allah bai gajiyar da mutum ba kai ba ka isa ka gajiyar da shi ba. Gwamnatin Al-makura mai adalci ne, a kowanne fanni. Balle haƙƙin wanda yayi aiki, wanda babu inda ya dogara sai ga Allah da kuma wannan kuɗin aikin a ce wai za a yi maka wasa da wannan? Al-makura baya wasa da wannan.
Don haka nake kira ga ma’aikata su ƙara haƙuri shi kuma mai gira Gwamna Umar Tanko Al-makura ya duba yanayin da aka shiga idan hakin a Gwamnatin jihar ce a fito fili a gaya masu domin a dawo masu da albashinsu kamar yadda ake biyansu baya.
Ni ɗin nan bari na gaya maka Allah ya sani shi ma ya sani na taɓa saminshi na ce, ranka ya daɗe yadda ka faro domin Allah. Tun 2011 kana yi tsakaninka da Allah da ma’aikin Allah, ka ci gaba a haka, mutum ba a iya masa, dole a samu masu son ganin kasawarka. Amma tunda Allah ya ce, ba za a ga kasawarka ba, karka damu da maganar kowa. Na san lokacin da na yi wannan magana akwai wasu mutanen da suke wajen, kuma idan suka karanta jaridar nan za su tuna cewa an yi haka.
Mu dai mukan bashi shawara daidai gwargwadon iyawarmu. Na san ni ba komai ba ne amma idan aka sameni kan batun abin da ya shafi wannan jihar mukan bada shawara daidai gwargwado.
Gwamnati ta ce za ta sayar da kadarorin gwamnati mallakar jihar dake faɗin ƙasar nan, wasu jama’a suna ta cece-kuce. Ko me za ka ce?
Duk waɗannan masu sukar gwamnati kan wannan ƙudurin iliminsu ne bai kai ba. Waɗannan kadarorin ba don gwamna Al-makura ya fito ya faɗi ba ai da dama mutanen jihar basu san dashi ba. Wasu ne ƙalilan suke moransu. Kuma abin da aka ce za a sanya a kasuwa to masu sukar su je su saya mana ai ko waye za a sayar masa.
Abin da bashi da amfani a gareka a wani jihar kamar Legas, Kaduna, Abuja, Jos kai ko a Lafia ne idan bashi da amfani ga jama’a sayar da shi a yi wa talaka aikin da zai amfaneshi ya fi, saboda babu asara.
Misali ;kaine kayi gidaje kamar 50 sai goma suka lalace sai ka sayar dasu sai a ce saboda meye ka sayar? Ya kamata idan mutum zai yi suka yayi bincike da a ce ana samun masu kishin Jihar Nasarawa kamar Al-makura da ci gaban da zamu samu yafi haka.
Wani ya ce, gwamna Al-makura yana burin yi wa Jihar tsirara ne. Me za ka ce?
Wanne shawara kake da shi ga al’umman Jihar Nasarawa?
Kullun muna kira ga al’umman jihar cewa babu abin da ya kai zaman lafiya daɗi, mu daina batun ƙabilanci da addini kada mutum yana neman biyan buƙatarsa ya riƙa sanya addini. Idan mutum yayi ibada ya yiwa kansa ne.
Wannan jihar tana buƙatar zaman lafiya, mu zauna lafiya, Shugabanci da mutum ya ke yi haƙƙin kowa na kansa. Mu manta da batun ƙabilanci.