Ina Jin Dadin Fitowa A Rol Din Muguwa – Saratu Gidado

Saratu Gidado

Daga Mukhtar Yakubu.

Matakin da fitacciyar jaruma Saratu Gidado take fitowa a matsayin muguwa a cikin fim shi ne ya ke zuwa zuciyar mutane a duk lokacin da aka ambace ta, domin kuwa tun daga lokacin da ta fara harkar fim da wannan rol din ta yi suna don haka ma ko a kan hanya aka gan ta to irin wannan kallon a ke yi mata. Wani abin mamaki da jaruma Saratu Gidado take da shi za a iya cewar ta rike Kambun ta domin tsawon lokacin da ta shafe ana damawa da ita, har yanzu jarumar ana yayin ta, sai dai har yanzu da dama mutane ba su san wacece Saratu Gidado ba, kuma ya aka yi ta samu sunan Daso?

A cikin tattaunawar su da wakilin mu jarumar ta fadi cikakken tarihin ta da kuma irin rawar da ta Kara wadda ta kai ta ga yin dogon lokaci ana damawa da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda hirar ta kasance.

Da Farko Za Mu So Ki Gabatar Da Kan Ki Ga Masu Karatun Mu

To Assalamu Alaikum, ni dai suna na Saratu Gidado, wadda aka fi sani da sunan Daso, kuma ni ‘yar asalin jihar Kano ce Bahaushiya a cikin birnin kano aka haife ni a shekarar 1968, kuma na yi makarantar firamare da Sakandare duk a Kano daga nan na je Kaduna Phonytacni in da na yi Diploma a kan abin da ya shafi harkar kasuwanci, sannan kuma akwai  makarantar da na je a Landan na yi wani kwas, bayan nan na yi koyarwa a makarantar firamare kafin daga baya na shiga harkar fim a shekara ta 2000 a yanzu ina ci gaba da harka ta ta fim kuma ina tare da mijina, alhamdulillah wannan shi ne kadan daga cikin tarihin rayuwata.

Da ya ke kin fadi shekarar da kika fara harkar fim ko za ki iya tuna fim din ki na farko da kika fara fitowa, da ma wadanda suka biyo bayan sa?

To ba zan manta ba fim din da na fara fitowa a cikin sa shi ne Feleke wanda kuma fitowa daya na yi a cikin sa, wanda Furodusa Ali Indabawa ya shirya  kuma shi ne ya hada ni da kamfanin Sarauniya a lokacin suna kan gani yar su, to su ne suka rinka saka ni a fim daga nan har duniya ta sanni.

Sunan da kika shahara da shi wato Daso ya aka yi kika same shi?

To shi wannan sunan dai suna ne da na fito da shi a cikin fim din Linzami da wuta, sai na fito a matsayin Daso, to daga nan wannan sunan ya bi ni har yanzu a ke kira na da sunan Daso .

Amma idan ba ki manta su ba za mu so ki fada mana wasu daga cikin finafinan da kike fito a cikin.

E to duk da an dauki lokaci mai tsawo sai dai na fadi wasu daga cikin su, kamar fim din da na yi na farko Feleke, sai Linzami da wuta,, Sansani, Kasko, Rawani, Garwashi, Kasar mu, amma da ya ke abin da yawa ba zan iya kawo su ba na manta, na baya bayan nan da na fito shi ne fim mai dogon Zango na Labarana.wadda na fito a matsayin Hajiya Babba wadda duk gidan ni a ke tsoro.

Kusan duk fitowar da kike yi a cikin fim kina fitowa ne a matsayin muguwa, ko ke ce kike zabar hakan?

To gaskiya ba zabi na ba ne, don ba zan manta ba, wanda ya fara ba ni wannan rol na mugunta shi ne Darakta Aminu Muhammad Sabo Allah ya ji kan sa, shi ne duk wani fim da zan yi musu, sai ya ba ni rol na mugunta Amma dai ban san dalilin ba ina ganin ko ya fi ganin na fi dacewa da wannan rol din ne shi ya sa ya ke ba ni. Amma dai iyawa ma tana sa a ba ka rol, domin ba kowa zai iya ba, don akwai wadanda idan an ba su daga sun fara sai su kasa to ina ganin yanayi na ya duba shi ya sa ya ke ba ni rol din.

To kina ganin wannan rol din bai bi ki ba a wajen masu kallo suna yi miki kallon muguwa?

A a bai bi ni ba domin ko a yau mai A daidaita Sahu, mashin mai kafa uku da ya dauke ni sai ya rinka mamaki, ya ke cewa, muna ganin ki a fim mai fada Amma yanzu ga shi muna ta hira da ke. Sai na ce masu wancan fim ne ba hali na ba ne abu ne da a ke rubutawa muna bin labarin kamar wanda za a ba shi Bindiga ya rinka Harbin mutane ai ka ga ba gaske ba ne, ko mutum ya fito a Dan sanda, ai ba shi ba ne to haka ba hali na ba ne rol ne kawai na fim.

Da alama dai ke ma kina Jin dadin fitowa a wannan matsayin na mugunta.

Ai har gobe ina son na fito kuma ina alfahari da fitowar da na ke yi a matsayin muguwa, don wasu ma cewa suka yi idan aka ba ni rol ba shi ba to ba ya dacewa da ni, don haka har yanzu, ko na fito a makirar suruka da zan rinka takura Dana ya saki matar sa ko muna zaune gida daya da matar Dana na rinka yi mata sharri, to gaskiya har yanzu ana ba ni rol din mugunta, kuma na fi jin dadin sa. Ai kamar Shu’aibu Lawan Kumurci ne, yanzu idan ka ce ya fito a matsayin Yaron kirki a fim ba zai iya ba, kawai a ba shi rol din maza kawai na harkar Daba, don haka ni ma na fi son na fito a rol din mugunta, ba sauki.

Baya ga harkar fim, kuma akwai wata Gidauniyar tallafa wa marayu da mabukata ta da kika samar ko za ki yi mana bayanin ta?

To abin da ya shafi Gidauniyar da na kafa dai na zaunu na ga harkar fim ita kadai na ke yi, kuma ina bukatar na samar da wani abu da zan rinka samun kudin da zan rinka gudanar da rayuwata bayan fim, don haka sai na kafa wani kamfani mai suna Daso Intertaiment wanda zan rinka samar da yadda zan rinka harkokin tallace tallace da kuma M C a wajen taro ko a wajen biki wanda duk harkar dogaro da kai ce, to kuma sai ya zama a wannan aikin nawa na samar da wani tsarin na taimakon mabukata musamman yara da iyayen su ba su da karfi da kuma marayu da almajirai, domin ina da burin taimakon mutane, wadda na ke ganin ni da wata babbar mai kudi ne to sai na fito neman wani muka I na siyasa wanda idan na ci zabe zan taimaka wa jama’a to Amma babu dama kuma babu daurin gindi, don siyasa sai ka san wani, to gaskiya ina da burin taimakon Jama’a na kauye da na birni, musamman a wannan lokacin da kullum masu bukatar sai karuwa su ke yi, don haka sai na samar da wannan kamfanin wanda a yanzu ina harkar gidan biki, kuma ina yin wasu guntayen fim ina sakawa a YouTube da sauran abubuwa wanda ta haka ne na ke samun kudin da na ke taimakon mabukata, kamar da Azumi kullum zan dafa abinci a gidana a rinka raba wa yara lokacin shan ruwa, sannan akwai tsarin bin kauyuka mai suna Door to Door, wanda mu ke kai musu abinci danye ba wanda aka dafa ba, kamar Shinkafa Masarada Doya da sauran kayan bukata, duk da ba za ka iya ciyar da mutane ba, Amma ko na rana daya ka dauke wa mutum a wani abu ne mai muhimanci.

Wannan harkar ciyarwa da kika fada sai muka ga kamar ta fi karfin aljihun kiko ta ina kike samun kudin gudanar da ita da ya ke yanzu harkar ta bunkasa?

To a baya dai da kudin hannuna na ke gudanar da harkar Amma daga baya da na ga abin yana nema ya gagara, sai na ke sanarwa a Social Media cewar muna neman taimako a kan manufar da mu ke da ita ta ciyarwa ga mabukata, to jama’a kuma suna bayar da gudummawar su sosai ana turo mana da kudi ta Banki da kuma kayan abinci wanda a ke turowa duk muna samu daga jama’a masu neman ladan ciyarwa, da haka mu ke samu mu ke gudanar da harkokin taimakon jama’ar da mu ke yi, kuma har yanzu kofar mu a bude take ga duk wanda ya ke bukatar ya taimaka wa mutane idan ya kawo za mu bi hanyoyin da suka dace don masu bukata su samu.

Idan kuma koma ga harkar fim da kike cikin ta, a matsayin ki na Dattijiwa a cikin harkar, ko wacce shawara za ki bai wa yara da su ke cikin harkar musamman mata.

To ni kiran da zan yi ga saba bin ‘yan fim, shi ne mu a zamanin mu har ga Allah matan da suka shigo da wadanda muka tarar irin su Abida Fati Muhammad, gaskiya a lokacin ba a shaye shayen kwayoyi kamar yadda yaran mu sababbi da su ke shigowa a yanzu ni dai shawara ta a gare su su sani’ ya mace uwa ce, za ki zama uwa nan gaba ki zama kaka kuma duk abin da kika yi tarihi zai ajiye, sai kin ji wata rana an fada wa ‘ya’yan ki ko jikokin ki, don haka kada dadin duniya da rudin kawaye ya sa ku rinka jefa kan ku cikin harkar shaye shaye, babu mutunci a cikin harkar, don haka mata a kiyaye.

To madalla mun gode.

Nima na gode sosai.

Exit mobile version