Abba Ibrahim Wada" />

Ina Koyi Da Ronaldo, Cewar Mbappe

Mbappe

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German Kylian Mbappe ya jinjina wa dan wasan da yake matuwar kauna, kuma yake kwaikwaya, Cristiano Ronaldo bayan da suka raba rana a wasan da kasarsa Farsansa ta fafata da Portugal a gasar Lig na kasashen Turai da suka tashi canjaras. 

Duk da kokari da dagewa da ‘yan wasan gaban biyu suka yi daga dukkan bangarori, an tashi wasan ba kare bin damo duk da cewa duka kasashen biyu sun kai hare-hare wanda yakamata ace an samu zura kwallo a raga.

Sai dai a yayin da ba a saka kwallo a raga ba, Mbappe da Ronaldo sun yi iya kokarinsu na kayatar da ‘yan kallo a wasan da kowannensu ya gwada bajinta da baiwar da Allah ya yi masa a filin kwallo.

Mbappe ya sha bayyana yadda ya ke kaunar Cristiano Ronaldo, inda bayan wannan wasa ma ya hau dandalin sada zumunta yana jinjina ga Ronaldo, har ma yake bayyana shi a matsayin abin koyi a gare shi.

“Ronaldo babban dan wasa ne wanda ya kashe kofuna da dama a duniya sannan kuma ya kafa tarihin lashe kyaututtuka a kungiyoyin daya bugawa wasa da kuma kasarsa ta haihuwa wadda a ya taimakawa ta lashe kofin nahiyar Turai,” in ji Mbappe

Ya ci gaba da cewa “Koda yaushe ina koyon wasu abubuwa daga wajensa saboda babban dan wasa ne wanda kuma ya iya tafiya da mutane haka kuma duk tsawon shekarun daya dauka yana buga wasa, amma har yanzu tauraruwarsa ta na haskawa a idon duniya”

A kwanakin baya dai dan wasa Mbappe ya bayyana cewa zai bar kungiyarsa ta PSG ta kasar Faransa kuma tuni aka fara danganta shi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid har ila yau Barcelona da Inter Milan da Liberpool suna bibiyarsa.

Exit mobile version