Ina Mutukar Alfahari Da Al’ummar Bichi Bisa Zaben Da Suka Yi Min Na Shugabanci Karo Biyu A Jere -Barden Bichi

Bichi

Daga Ibrahim Muhammad,

A tsarin shugabanci na siyasa damace da ake samu daga al’umma ta yarda ko amincewarsu da Mutum bisa kulada halayyarsa da kuma irin mu’amala da yanda yake nuna kishi ga al’umma ta kyautatawa ko wucewa gaba dan ganin  cimma bukatar cigabansu.

Irin gudummuwa da ake gani wasu daidaiku ke bayar wane ke sawa al’ummarsu kan jawosu su matsanta musu su shiga harkokin siyasa domin tananne za su fadada irin taimako da suke a cikin al’umma.

Alhaji Sani Mukaddas Barden Bichi shi ne zababben shugaban karamar hujumar Bichi har karo biyu wanda yana daga cikin yan siyasa da tun farko al’ummar Bichi suka amince da irin kyakkyawar mu’amalarsa garesu da kishin son cigaban al’ummar Bichi dan haka  suka goyi bayan ya shiga siyasa dan bada gudumnuwa ga cigaban al’ummarsa.

Ga al’umnar Bichi sun tabbatar da cewa laya ta yi kyan rufi, domin kuwa zamewar Alhaji Sani Mukaddas shugaban karamar hukumar zababbe har karo biyu ya kawo musu tsare-tsare daya dada fadada cigaban karamar hukumar ta Bichi a bangarori da dama na cigaban al’umma.

A tarihin shugabancin karamar hukumar ba’a taba samun wani zababben shugaba da aka zabe shi karo biyu a jere ba sai Barde. Duk da wasu a baya sun yi shugabancin yankin Bichii amma shi ne kadai zuwa wannan lokaci al’umma suka zabe shi bisa amincewar kuri’unsu suka kara a matsayin zababben shugaba a jere sau biyu wamnan alama ce ta gansuwa da shi.

Irin ayyuka da Alhaji Sani Mukaddas ya aiwatar  a dukkan mazabbun Bichi guda 11  ta bangarori daban-daban a bayyane suke da ake gani a taba da cin moriyarsu,kama daga ginin dakunan shan magani da makarantu na boko dana islamiyya da asibitoci da hanyoyi da samar da rijiyoyi da kuma tallafa wa cigaban aikin noma da bunkasar kasuwanci a karamar hukumar. Dinbin daruruwan matasa da iyaye mata  ba za su manta da irin horon koya masu ayyukan sana’oi na  dogaro da kai  da basu  tallafin jari da Barde ya rikayi a lokuta daban-daban ba, yawancinsu da suka amfana na cigaba da bunkasa a sana’o’in kansu suna kuma amfanar da wasu a karkashinsu.

Duk wanda ya san yanayi da Bichi take a baya kafin zaman Barde shugaban karamar hukumar ta ya kwatantata da yadda ta zama wajen bunkasa  a zamanin Alhaji Sani Mukaddas zai tabbatar an sami gagarumin sauyi an kawatata da gine gine da hanyoyi da samar da yanayi da za ta iya ginuwa akan cigaba mai dorewa.

Abinda al’ummar Bichi suke alfahari da shi game da dansu Alhaji Sani Mukaddas shine na zamansa a tare da su koda yaushe yana karamar hukumarsa bai taba gudarsu ba  idan baya gida a Bichi  yana ofis in baka same shi ba  to kuwa ya tafi wani aiki na al’ummane Kano ko wajen jihar Kano  da dalilin kawo  aikin cigaban al’ummarsa.

Barden Bichi Alhaji Sani Mukaddas ya shaida mana cewa abinda yake jin dadi da alfahari da shi shi ne irin.kauna da aminci da goyon baya da al’ummar karamar hukumar Bichi suka nuna masa ta zabarsa har karo biyu a jere Kuma ya samu hadin kansu wajen aiwatar da ayyuka a bangarorin cigaba da dama.

Ya ce babban burinsa daya cika kafin ya bar mulki shi ne na samarwa da garin Bichi Mayanka na zamani, kuma cikin yardar Allah an riga kammala aikin ginata abin farin ciki ne da zai taimaka  ta fuskar bunkasa tallalin arzikin yankin.

Ya ce abin farin ciki a gare shi bayan yin zamani da Sarakuna Biyu tun daga lokacin da aka kirkiri masarsutar Bichi danban  akwai zababben dan majalisarsu na tarayya wanda shi ne daraktansa da ya yi masa yakin neman zabe Alhaji Abubakar Kabir kuma ya yi nasara wanda kuma yanzu haka yake kawowa Bichi ayyuka da ba’a taba samun wani dan majalisar tarayya a baya da ya yi wa Bichi ayyuka na cigaba da kula da al’umma da yake  ba.

Alhaji Sani Mukaddas wanda a zamanin mulkin sane aka sami masarautar Bichi ya zauna da sarki na farko a masarautar Alhaji Aminu Ado Bayero Sannan bayan an mayar da shi sarkin Kano aka nada dan’uwansa Alhaji Nasiru Ado Bayero da yanzu haka shi ne Sarkin Bichi.

Alhaji Sani Mukaddas ya ce ba shi da bakin irin godoya da zai yiwa al’ummar Bichi sai dai Allah ya saka musu da alkhairi tun daga kan malaman addini da yan boko manyan ma’aikata da kanana da iyayen kasa sarakuna da dagatai da hakimai da ‘yan kasuwa da dukkan sauran bangarorin al’umma  maza da mata da ‘yan siyasa  bisa hadin kansu gare shi. Kuma yana fata za su baiwa sabon shugaban karamar hukuma daya  gajeshi hadin-kai da goyon baya.

Alhaji sani Mukaddas ya ce, shi a zuciyarsa bai riki kowa da wani laifi da ya yi masa ba kuma yana rokon duk wanda ya batawa yi wa wani laifi cikin sani ko rashin sani ya yafe masa. Sannan ya godewa Gwamnan Kano Dokta Abdullahi Ganduje bisa goyon baya da ya bashi  tare da Kwamishinan kananan hukumomi Alhaji Murtala Sule Garo bisa hadin-kai da ya bashi wanda da hadin kansa ne ya sami nasarar gudanar da ayyuka.

Barden Bichi ya ce zai cigaba da bada goyon baya da biyayya ga Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje dan tabbatarda nasarar jam’iyyarsu ta APC a kowane mataki.

Exit mobile version