Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Ina Neman Kotu Ta Yi Min Adalci –Dakataccen Shugaban CAF

by Muhammad
January 8, 2021
in WASANNI
2 min read
CAF
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika ya bayyana cewa yana neman kotu ta masa adalci sakamakon dakatarwar da hukumar kwallon kafa ta duniya ta yi masa game da zargin cin hanci da rashawa a hukumar da yake rike da ita.

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar, Ahmad Ahmad na tsawon shekaru biyar bayan samun sa da laifukan almundahanar kudade da kuma karvar rashawa.

samndaads

Cikin sanarwar da FIFA ta fitar a shekarar dat a gabata ta ce Ahmad Ahmad dan asalin kasar Madagascar, zai kuma biya tarar dala dubu 220, baya ga haramcin na shiga harkokin gudanarwar wasannin na Afrika har tsawon shekaru biyar.

Tun a watan Maris din shekarar 2017 ne Ahmad Ahmad ya yi nasarar darewa kujerar shugabancin hukumar ta CAF yayin da kuma yake neman wa’adi na biyu a wannan shekarar ta 2021 da muka shiga.

Tuni Ahmad Ahmad mai shekaru 50 ya daukaka kara kan hukuncin na FIFA a kotun sauraren kararrakin wasanni ta CAS inda ya bukaci kotun dayi masa adalci ta hanyar janye masa adadin shekarun ko kuma rage masa.

Ko a cikin watan Afrilun bara, tsohon jami’in hukumar ta CAF Mista Fahmy ya aike wa FIFA wasikar da ke zargin Ahmad Ahmad da karkatar da wasu kudaden karvar rashawa da kuma cin zarafi da muzguna wa jami’an hukumar musamman mata, matakin da ya kai ga kame shi watanni biyu bayan zargin yayin gasar kwallon kafar mata da ta gudana a Faransa amma kuma aka sake shi kwana guda bayan kamen.

Dama dai bukatar Ahmad Ahmad ta ci gaba da jagorancin CAF ya gamu da kakkausar suka daga shugaban hukumar kwallon kafar Senegal Augustine Senghor, yayin da shugaban hukumar kwallon kafar Mauritania Ahmed Yahya da Jackues Anouma na Ivory Coast kana attajirin Afrika ta kudu Patrice Motsepe dukkanninsu suka nuna bukatar tsayawa takara don neman kujerar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda Ake Fafatawa A Gasar Afrika Ta ‘Yan Kasa Da shekara 17

Next Post

Ronaldo Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare

RelatedPosts

Pochettino

Pochettino Ya Kamu Da Cutar Korona

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya...

Solkjaer

Ban Damu Da Jita-Jitar Korata Daga Manchester United Ba, Cewar Solkjaer

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer...

ozil

Dole A Yiwa Ozil Hakuri – Zidane

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real...

Next Post
Takalmin Zinare

Ronaldo Ya Lashe Kyautar Takalmin Zinare

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version