Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Ina Ruwan Biri Da Gada?

by Sulaiman Ibrahim
March 17, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Ina Ruwan Biri Da Gada?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Ibrahim Yaya

Duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum, ya ga yadda a shekarar 2019 da ta gabata, wasu bata-gari suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al’umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai hari kan mai uwa da wabi, da cin zarafin ’yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al’umma, al’amuran da suka kasance ayyukan ta’addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa.
Amma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba. Wai duk da sunan ‘yanci na demokiradiya.
Kamar kowa ce kasa mai cikakken ’yanci, ita ma kasar Sin tana da ’yancin kafa dokokin da za su dace da yanayi da ma tsarin tafiyar da cikakkun yankunanta.
Wannan ya sa a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta kafa, da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong. A wannan karon kuma, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, ta amince da inganta tsarin dokar zaben yankin na Hong Kong, inda daga yanzu, masu kishin kasa ne kadai za su gudanar da harkokin zaben yankin.
Sai dai kamar kullum bayan aiwatar da wannan doka, ’yan ga ni na iya da da ’yan barandan kasashen yamma masu neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, suka fara nuna adawa da wannan doka, amma bakin alkalami ya riga ya bushe. Kuma mai daki, shi ya san inda ya ke masa Yoyo. Yankin Hong Kong wani bangane na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba. Harkokin Hong Kong, harkokin ne da suka shafi cikin gidan kasar Sin. Babu wata kasa da take da ikon tsoma baki a cikinsa, domin yin haka, ya saba ka’idoji da ma alakar kasa da kasa.
Abin tambaya shi ne, wai irin wadannan kasashe dake adawa da dokar zaben yankin Hong Kong na kasar Sin, ba su da dokokin zabe a kasashensu ne ko kuma? Da ma an ce, Gwano ba ya jin warin jikinsa.
Duk wata kasa mai cikakken ’yanci, wajibi ne tana da dokoki da suka dace da yanayin kasarta. Kuma duk wanda ya karya doka,ya kwana da sanin cewa, doka za ta taka shi. “Icce aka ce, tun yana danye ake lankwasa shi”. (Ibrahim Yaya)

SendShareTweetShare
Previous Post

Mata ‘Yan Kabilar Uygur Sun Karyata Rahotannin Karya Da Kafofin Watsa Labaran Kasashen Yamma Suka Bayar Kan Xinjiang

Next Post

Sanarwar Da Amurka Da Japan Suka Fitar Kan Sin Almara Ce Kawai

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by Sulaiman Ibrahim
19 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Sanarwar Da Amurka Da Japan Suka Fitar Kan Sin Almara Ce Kawai

Sanarwar Da Amurka Da Japan Suka Fitar Kan Sin Almara Ce Kawai

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version