Wakilinmu a Benin, Jihar Edo, Abdulrahman. A Masagala, ya tattauna da wani dattijo da ya shafe shekara 45 yana sana’ar sayar da goro. Al’amarin ya bunkasa, domin kuwa Malam Muhammadu bai tsaya a Arewa ba kadai har ya nausa Kudu. Bai tsaya nan ba, a wannan tattaunawar ya kuma fayyace yadda zaman Kudu yake tare da kwatantawa da ana Arewa. Ga cikakkiyar hirar:
LEADERSHIP A YAU: Da farko munason mu san sunanka?
MUHAMMADU GIDAN MADI: Sunana Muhammadu Gidan madi na haura shekaru saba’in a duniya kuma sana’ar sayar da goro nake yi tun ina yaro domin sana’ar da na samu ake yi agidanmu ke nan.
LEADERSHIP A YAU: Ka ce wannan sana’ar da ita ka bude ido ya kai kimanin shekara nawa kake cikin wannan sana’ar.
MUHAMMADU GIDAN MADI: A gaskiya na dade da na fara wannan sana’ar atakaice a yanzu haka akalla ba akasara ba ya kai kimanin shekaru arbain da biyar, domin tun ina gida Sakwato ina tasowa daga kauyenmu Gidan madi in bi ‘yan kasuwa zuwa nan kurmi in saya wannan goron in koma da shi Arewa, daga kasar Yarbawa har ya kai na dawo da zamana a nan cikin Kurmi kuma na zauna a yankuna daban- daban a nan kudanci daga bisani sai na yanke shawara na dawo da zamana a nan cikin garin Benin Jihar Edo.
LEADERSHIP A YAU: Ka ce ka dawo da zamanka a nan Benin ko yaya kake samun goron a nan din.
MUHAMMADU GIDAN MADI: Ai ita sana’a idan ka sa kanka kuma kana son ka yi ta, wannan abu ne mai sauki, saboda haka zuwa nake yi kasar Yarbawa in sayo in sa a mota akawo man a sauke sannan sai in ci gaba da sayarwa kamar yadda na saba.
LEADERSHIP A YAU: Da yake Allah ya yi maka tsawon rai ka ga jiya ka ga yau a cikin zaman da ka yi a nan kudanci yaya za ka kwatanta yanayin zaman Arewa da kuma a nan kudanci ta bangaren rayuwa, a matsayinka na kai dan Arewa mai zama a nan Kudu?
MUHAMMADU GIDAN MADI: Ai ni a ganina Nijeriya duk daya take a wurina, babu wani banbanci da ya taka kara ta karya, domin duk inda kake idan kana rike gaskiya to za ka zauna lafiya da kowa, sai dai abin da zan iya ce wa, lallai gida gida ne amma banda wannan babu wani abu na daban musamman a mu Hausawa mazauna a nan jihar Edo, muna da kyakkyawar alaka ta zamantakewa da kabialar jihar ba ma samun matsala.
LEADERSHIP A YAU: Ka ce akwai kyakkyawar mua’amila a tsakaninku da kabilar jahar ko akwai batun auratayya tsakaninku da su kamar yadda ake yi da na Arewa?
MUHAMMADU GIDAN MADI: Kwarai da gaske sai ma ince kusan ya fi na Arewar, domin na Arewa saboda mun bude ido mun samu yanki daya muka tashi wasu al’adun ma suna shigar juna amma wadannan idan muka yi la’akari ai ba mu tashi tare ba. Al’adu kuma sun sha bamban amma duk da wannan suna ba da amanna da mu suna ba mu ‘ya’yansu mata muna aurensu kuma ana zaman lafiya ga kuma son addini gare su muddin ana ci gaba da nuna musu suna kulawa sosai kuma a cikinsu ma akwai maluma da masu haddan Kur’ani domin suna da makarantu na Musuluci da dama a jihar nan tasu.
LEADERSHIP A YAU: Ko kai ma ka samu an ba ka ka aura daga cikin ‘ya’yansu mata kamar yadda ka yi bayani?
MUHAMMADU GIDAN MADI: A’a, agaskiya ni dai Allah bai nufe ni na samu na aure su ba, amma ‘yan Arewa da dama sun aure su, kuma sun samu zuri’a da su, kuma suna zaune lafiya da su domin su mutane ne masu jimiri da duk wata wahala a gidan mijinsu na aure.
LEADERSHIP A YAU: A nan zamanka na Kudu kana tare da iyalinka ne ko kuma ka bar su a gida Arewa?.
MUHAMMADU GIDAN MADI: Ai ina tare da su a nan, sai dai wasu daga cikin ‘ya’yana suna karatu ne a Arewa domin ina da ‘ya’ya sun kai su tara kuma ina da jikoki tsakanin maza da mata sama da ashirin.
Wace shawara ko kiran kake da shi wa al’umman Arewa mazauna Kudu da na gida Arewa?
Kiran da zan yi shi ne su hada kansu su mance da irin bambance- bambance da ke tsakaninsu da juna ko da wasu kabilu kowa ya rungumi sana’a da kuma noma domin muddin sun rungumi wannan abu guda biyu to babu shakka za a kori talauci da yunwa.