Ina Son Barin Real Madrid Har Abada, Inji Contrao

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Fabio Contrao wanda yake zaman aro a kungiyar kwallonj kafa ta Sporting Lisbon ya bayyana cewa yanason yabar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid gaba daya a karshen kaka.

Contrao, wanda yakoma Real Madrid a shekara ta 2011 daga kungiyar kwallon kafa ta Benfica wadda itama  take kasar Portugal yace abune mai wahala barin kungiya kamar Real Madrid saboda irin girmanta da tarihinta.

Ya ci gaba da cewa lokacin da yakoma kungiyar yayi farin ciki a rayuwarsa domin yasan cewa yaje makura a wasan kwallon kafa saboda haka baya bukatar komai sai dagewa domin samun buga wasanni.

Sai dai yace daga baya abubuwa suka dinga tafiya ba dai-dai ba na jin ciwo da kuma abubuwan da suka saka yasamu matsala dayawa ta rashin buga wasa a kungiyar.

Ya kara da cewa yana farin ciki a kungiyar dayake a yanzu ta Sporting Lisbon kuma baya fatan barin kungiyar sai dai bazai taba nuna farin cikinsa ba idan Real Madrid tayi rashin nasara a kowanne wasa saboda kungiyar tayi masa komai kuma bazai taba mantawa da ita a rayuwarsa ba.

Contrao dai yabuga wasanni 43 ne a kungiyar tun bayan komawarsa kungiyar a shekara ta 2011 sannan kuma ya wakilci kasarsa ta Portugal a wasanni daba-daban da suka gayyace shi.

 

Exit mobile version