Abba Ibrahim Wada" />

Ina Son In Yi Ritaya A Barcelona

Matashin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ansu Fati, ya bayyana cewa babban burinsa yanzu a duniya shine ya kammala buga kwallo a Barcelona bayan ya kafa manya manyan tarihai.

Duk da cewa shekararsa 17 a duniya, tuni dan wasa Ansu Fati ya zura kwallaye biyu a wasanni uku da aka fara bugawa dashi sannan kuma ya shigo wasanni sau shida bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Duk da cewa akwai kungiyoyin da suke bibiyarsa suke ganin kamar nan gaba zai iya zama babban dan wasa a duniya idan ya sake girma sai dai tuni matashin dan wasan ya yanke shawarar cigaba da zama a Barcelona har karshen rayuwarsa ta kwallo.

“Zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta Osasuna dana fara a rayuwa babban tarihi ne wanda na dade ina mafarki da kuma kwallon dana zura a ragar Balencia a filin wasa na Nou Camp duka bazan taba mantawa dasu ba” in ji Ansu Fati

Ya cigaba da cewa “Babban burina shine cigaba da kasancewa a wannan kungiyar har karshen rayuwa ta kuma inason in kafa tarihin lashe kofuna da cin kwallaye da kuma uwa uba samun kyaututtuka a matsayina na dan kwallo”

Tuni dai shugabannin kungiyar ta Barcelona suka fara tattaunawa da dan wasan da wakilansa domin ganin matashin dan wasan ya sake kulla sabuwar yarjejeniya dasu wanda hakan zai hana manyan kungiyoyi zawarcinsa.

Exit mobile version