Ina Son Kafa Tarihi A Real Madrid -David Alaba  

Alaba

Kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta cimma yarjejeniya da tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, David Alaba domin ya buga mata wasa na tsawon kakar wasanni biyar kuma kungiyar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na internet ranar Juma’a.

 

A cewar Real Madrid,  za’a kaddamar da dan wasa David Alaba a matsayin sabon dan wasan Real Madrid bayan kammala wasannin European Championship a watan gobe wanda kasarsa ta Austria zata fafata.

 

Yana zuwa Real Madrid ne kwana guda bayan kocinta Zinedine Zidane ya sauka daga mukaminsa sakamakon rashin daukar ko da kofin shayi ne a kakar wasa ta 2020 zuw 21 da aka kammala.

 

David Alaba,  dan kasar Austria da ke tsaron baya ya je Bayern Munich ne a shekarar 2008  kuma dan wasan  mai shekara 28 a duniya, ya taimaka wa Bayern wajen daukar kofin Champions League a shekarar 2013 da 2020.

 

Dan wasan ya buga wasanni 431 a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich tsawon shekaru 13 da ya kwashe a kungiyar da ke buga gasar Bundesliga kuma ya lashe kofuna daban-daban a zaman da yayi a Jamus din.

Exit mobile version