Ina Son Karawa Da Anthony Joshua –David Haye

Tsohon dan damben duniya, David Haye ya ce yana son karawa da Anthony Joshua a babban wasan damben da za a yi a shekara mai zuwa.

Dabid Haye, wanda a halin yanzu yake murmurewa daga raunin da ya samu a dokewar da Tony Bellew ya yi masa a watan Maris din wannan shekarar, wanda akwai maganar sake fafatawa a junansu a watan Disamba.

Haye ya ce yana son haduwa da Anthony Joshua domin ya san babbar karawa ce matukar suka hadu, kuma za su kayatar da ‘yan kallo.

“Yanzu abin da yake gabana shi ne warkewa kuma na fada tun lokacin da aka yi min aiki, wannan shi ne a gabana. Akwai fafatwa da mutane da dama da ake magana a kai, amma har yanzu ban shirya ba. Ita ma maganarmu ta sake fafatawa da Tony Bellew tana nan amma idan duka muka amince.” In ji Haye.

Haye ya kara da cewa, “idan har zan iya samun wasanni biyu, zan iya shiryi na musamma a karawata da Joshua”

Anthony Joshua dai zai fafata wasansa na gaba da Kubrat Puleb a ranar 28 ga watan Oktoba.

Exit mobile version