Mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester united, jose mourinho yace yanason watarana ace yana koyar da tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa.
A yayin hirarsa da manema labarai a birnin Manchester, mourinho yace abune mai kyau acewatarana yana koyar da wata ƙasar kuma ya fafata a gasar cin kofin duniya.
Ya cigaba da cewa aikin koyar da ƙungiya aiki ne mai wahala domin kullum kana cikin tunanin yadda zaka fito a wasan gaba kuma kana tunanin dan wasanka yaji ciwo ko kuma an dakatar dashi.
Ya ƙara da cewa koyar da wata ƙasar abune mai sauƙi domin sai bayan kusan watanni biyu sannan zaka fara tunanin ƙwallo saboda ba koda yaushe ake buga was aba.
Sannan ya laseh kofuna 25 a tarihinsa ciki har da kofin zakarun nahiyar turai guda biyu da yaci a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC.Porto da inter millan.