Ina Son Lashe Kofin Zakarun Turai A PSG – Ramos

Ramos

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Sergio Ramos, ya bayyana cewa zaiso ace ya taimakawa kungiyar tasa domin lashe gasar cin kofin zakarun turai kafin ya bar kungiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain ta dauki dan wasa Sergio Ramos kan kwantaragin shekara biyu bayan karewar zaman dan wasan a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a karshen watan daya gabata.

Ramos mai shekara 35 ya bar Real Madrid ne bayan karewar zamansa na shekara 16 a karshen watan Yuni kuma dan wasan da ya fi ko wanne dan wasa buga wasa a Sifaniya ya ci kofunan La Liga guda biyar da kofin zakarun turai na Champions league guda hudu.

Ramos ne dan wasa na uku da PSG ta dauka a wannan kakar bayan dan wasan Morocco Achraf Hakimi daga Inter Milan da kuma Georginio Wijnaldum dan kasar Netherland wanda ya koma PSG a matsayin kyauta bayan karewar kwantaraginsa a Liberpool.

Kungiyar da Mauricio Pochettino ke jagoranta da suka gaza cin kofi a kakar bara, tana neman mai tsaron ragar Italiya Gianluigi Donnarumma, wanda ya bar AC Milan kuma baya kammala gasar Euro ake saran zai saka hannu a PSG din.

Ramos wanda ba a tafi da shi gasar Euro 2020 ba, zai hadu da tsofaffin abokansa da suka yi Real Madrid tare Angel di Maria da Keylor Nabas sannan zai hadu da abokin hamayyarsa Neymar.

Dan wasan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa PSG ce wurin da mutum zai ci gaba da tafiyar da burinsa, kungiyar da za su ci gaba da samun nasara za su ci gaba da fafatawa a PSG.

A ranar Talata 15 ga watan Yuni ne Real Madrid ta sanar cewar Kyaftin dinta Sergio Ramos zai bar kungiyar da zarar yarjejeniyarsa ta kare a karshen watan Yuni kuma Ramos, mai shekara 35, ya lashe kofuna da yawa a Real Madrid ciki har da La Liga biyar da Champions Leagues hudu, tun bayan da ya koma kungiyar daga Sebilla a shekarar 2005.

Mai tsaron bayan ya buga wa Real Madrid wasanni 671 da cin kwallo 101, wanda kwantiraginsa ya ya kare a karshen watan Yuni sannan ya lashe kofin duniya da kofunan nahiyar turai guda biyu a tawagar kasar Spain.

Exit mobile version