Ina Son Mbappe Ya Ci Gaba Da Zama A PSG –Neymar Jnr

Neymar Jnr

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar Jnr, ya bayyana cewa baya fatan dan wasa Mbappe yabar kungiyar ta PSG domin suna bukatarsa a kungiyar a halin yanzu.

A satin daya gabata ne shugaban kungiyar, Nasser Al-Khelaifi ya bayyana cewa dan wasa  Kylian Mbappe zai ci gaba da buga wasa a Ligue a ya yinda yake  mayar da martani kan rade-radin da ake yi kan makomar dan wasan tawagar Faransan a PSG.

Mbappe, wanda ya ci kwallo 42 a dukkan fafatawa a kakar nan a PSG, yana da sauran yarjejeniyar da za ta kare a karshen watan Yunin shekara ta 2022 kuma ana ta alakanta dan kwallon tawagar Faransan da cewar zai koma Real Madrid da buga wasa daga kakar wasa ta badi.

”Bari na fayyace, Mbappe zai ci gaba da wasa a Paris, ba za mu sayar da shi ba, ba za mu bari ya bar PSG a matakin wanda bai da yarjejeniya da mu ba” Al-Khelaifi ya sanar wa da jaridar L’Ekuipe

Ya kara da cewa Mbappe yana da dukkan abubuwan da yake bukata a Paris saboda haka ina   kuma zai je? wacce kungiyace a matakin cimma buri da za ta yi kafada da PSG a wannan lokacin?

Ya ci gaba da cewa “Abin da zan ce komai yana tafiya yadda ya kamata, ina fatan zamu kulla sabuwar yarjejeniya da shi nan gaba kadan kuma hakan zai rufe bakin duk wani labarin cewa zai tafi daga PSG”.

”Nan birnin Paris ne, kuma kasarsa ce, yana da abinda ya sa a gaba, ba kawai kwallon kafa ba, har da daga darajar gasar Ligue 1 da kasarsa da kuma birninsa wanda bashi da wanda ya fishi a duniya.” Al-Khilafi ya sake bayyanawa

PSG ta kammala kakar bana da kofi daya shi ne French Cup, bayan da ta kasa lashe Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille, wadda ta ci kofin bana an kuma yi waje da PSG daga gasar Champions League a karawar daf da karshe a bana, bayan da ta kai wasan karshe a bara da Bayern Munich ta yi nasara da ci 1-0.

Exit mobile version