Abba Ibrahim Wada">

Ina Son Mu Sake Lashe Kofuna Uku A Wannan Sabuwar Kakar – Lewandowski

Soccer Football - Bundesliga - Schalke 04 v Bayern Munich - Veltins-Arena, Gelsenkirchen, Germany - August 24, 2019 Bayern Munich's Robert Lewandowski celebrates scoring their third goal and completing his hat-trick REUTERS/Ralph Orlowski

Ina Son Mu Sake Lashe Kofuna Uku A Wannan Sabuwar Kakar — Lewandowski
dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Robert Lewandowski, ya bayyana cewa yana fatan a sabuwar kakar wasan da aka fara kungiyar tasa ta sake lashe kofunan data lashe a kakar data wuce.
A ranar Alhamis ne kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lashe gasar Super Cup bayan doke kungiyar Sebilla ta kasar Sipaniya da kwallaye 2-1 a daren Alhamis, ya yin fafatwar ta kai su ga karin lokaci na mintuna 30, bayan kammala mintuna 90 na al’ada suna kunnen doki 1-1.
Sebilla ce ta soma jefa kwallo a ragar Bayern Munich ta hannun dan wasanta Lucas Ocampos a bugun fanareti, kafin daga bisani Leon Goretzka na kungiyar ta Munich ya maida wasan 1-1, ya yinda kuma a mintuna 104 na karin lokaci dan kasar Sipaniya Roberto Martinez da ya maye gurbin Goretzka ya jefa kwallo ta biyu a ragar Sebilla.
Gasar ta Super Cup dai itace ta hudu da kungiyar Bayern Munich ta lashe a wannan shekara, haka zalika tana da damar lashe karin ta 5 a ranar Laraba mai zuwa inda za ta fafata ta Borussia Dortmund, abokiyar hamayyarta a gasar Super Cup na kasar Jamus.
Ana dai fafata wasan lashe gasar Super Cup ne tsakanin zakarar gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League da kuma zakarar gasar Europa sai dai wani abu kuma daya dauki hankali shi ne baiwa ‘yan kallo kimanin dubu 15 da 500 damar shiga filin wasan na Super Cup da ya gudana a birnin Budapest na kasar Hungray.
Bayan tashi daga wasan ne dan wasan gaban na Bayern Munchen, Robert Lewandowski ya nuna sha’awarsa na ganin kungiyar tasa ta sake lashe kofunan zakarun turai dana Bundesliga da duk wani kofi da kungiyar ta lashe a bana.

Exit mobile version