Connect with us

WASANNI

Ina Son United Ta Sayo Bale —Nebille

Published

on

sohon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Gary Nebille ya bayyana cewa burinsa a yanzu shi ne ya ga dan wasan Real Madrid Gareth Bale ya koma Manchester United.

Bale dai ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar ta Real Madrid a ranar da kungiyar ta doke Liberpool a wasan karshe na cin kofin zakarun turai wasan da dan wasan ya zura kwallaye biyu a raga.

Sai dai mai koyar da yan wasan na Manchester United Jose Mourinho bayason kungiyar ta kashe kudin da ta ware domin siyan yan wasa a kan dan wasa guda daya bayan da aka bayyana cewa kungiyar Real Madrid zata bukaci kusan fam miliyan 200.

Tun a shekarar data gabata ne dai aka fara danganta Bale da komawa Manchester United sannan kuma tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham wadda ya bari zuwa Real Madrid ita ma ta nuna tana son ya koma kungiyar.

Gary Nebille ya bayyana cewa burinsa shi ne ya ga manyan yan wasa irinsu Ronaldo da Messi da Neymar suna bugawa kungiyar wasa saboda haka idan kungiyar ta sayi Bale zai canja kungiyar zuwa babbar kungiyar.

Bale dai yanada ragowar shekaru hudu a Real Madrid bayan daya sake sabon kwantaragi a farkon wannan kakar sannan ya buga wasanni 39 kuma ya zura kwallaye 21 a wannan kakar duk da cewa bai samu buga wasanni da yawa ba a kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: