Connect with us

LABARAI

Ina Takaicin Gaza Kare Rayukan Katsinawa, In Ji Masari

Published

on

Aminu Masari, Gwamnan Jihar Katsina yace ya Gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar game da ta’addancin ‘yan bindiga

A yayin zanta warsa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, yace yana cikin matukar bakin ciki ganin yadda mutane ke cikin hali mawuyaci tun zuwanshi a matsayin gwamna.
Yace ‘yan ta’addan ” gwara dabbobi dasu” saboda kawai kisa suke ba dalili ba wariya.
“Bansan me zangayawa mutane ba, bazan iya hada fuska dasuba, saboda nagaza karesu, sabanini alkawarorin da muka dauka nakasa cewa, zamu kare lafiyarsu, rayukansu da dukiyoyinsu.” Ya fada hakan.

“Bantaba sanin halayyar mutane dake zaune cikin dajika ba, ‘yan bindiga, wadanda halayyarsu tafi muni akan dabbobi. A daji Zaki ko Damisa suna kisane kawai lokacin dasuke jin yunwa, kuma ba kisa zasuyi tayi ba, kawai zasu kashe dai-dai wacce zasu cine kawai a lokacin.”
“Amma abinda muke gani anan shine, ‘yan bindiga zasu shigo gari suyi ta harbi kan mai uwa dawabi, kuma ba’asan meyasa suke haka ba. Kamar yadda sukayi kwanan nan a Faskari da wani sashi na karamar hukumar Dandume.Ta yaya Dan Adam zaiyi halayyar da ko dabba bazatayiba?”

“Aikin mu shine mu kara taimakawa Jami’an tsaro, wanda na tabbatar munayi sama da kashi 90% akan duk abinda suka bukata, gwargwadon abinda ke hannunmu.” Ya fada hakan.
Masari yafada hakan ne a yayin maida martani ga maganar da zauren dattawan Arewa suka futar cewa, shugaban kasa da gwamnoni sun gaza sauke nauyin dake kansu wajen kare rayuka.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: