Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo, da ya kafa sabon tarihin zura kwallaye 750 bayan kwallonsa ta ranar Laraba a ragar Dynamo Kyib yayin wasannin cin kofin zakarun Turai, kuma Ronaldo ya ce fatansa shi ne nan gaba kadan ya cike yawan kwallayen da ya zura zuwa 800.
Ronaldo mai shekaru 35 a duniya wanda ya zura kwallaye 450 a tsawon buga wasansa a Real Madrid, ya kuma zura kwallaye 118 a zamansa a Manchester United baya ga wasu kwallayen 102 ga kasarsa ta Portugal sai kuma 75 ga sabuwar kungiyarsa da ya ke buga wasa a yanzu wato Juventus sannan tsaffin kwallaye 5 da ya zura a kungiyarsa ta farko wato Sporting Lisbon ta Portugal.
A sakon da ya wallafa a Shafinsa, Ronaldo, ya yabawa kungiyoyin da ya buga wasa a cikinsu wanda ya kai shi ga zura yawan kwallayen, dama abokanan hamayyarsa daban-daban wadanda ya ce sune suka kara masa kaimi wajen ganin ya zura kwallayen ya yinda ya yiwa magoya bayansa alkawarin cewa yanzu abin da ke gabansa shi ne ganin ya kara yawan kwallayen nasa zuwa 800.
“Inason ganin na kai tarihin zura kwallo 800 a raga domin kafa babban tarihi saboda haka nasan akwai aiki a gabana na zura kwallaye 50 nan gaba sai dai nasan kamar yadda na dage na jure na zura wadancan na baya wannan ma ba zata gagara ba” in ji Ronaldo
Mintuna kalilan bayan zura kwallon ta Ronaldo a daren laraba dai, hukumar UEFA ce farkon taya dan wasan murna inda hukumar ta bayyana Ronaldo a matsayin gwarzo wanda kuma hukumar ba zata taba mantawa dashi ba a duniya kuma ya shiga cikin tarihinta
Yayin wasan na Juventus a Larabar data gabata dan Fedrico Chiesa ne ya fara zura kwallo wadda ke matsayin irinta ta farko da ya zura karkashin gasar cin kofin zakarun Turai, sai kuma Albaro Morata ya zura kwallo ta biyu.