Akalla Mutane sama da 57,000 suka tserewa gidajen su daga tsibirin Bali da ke kasar Indonesiya domin kaucewa aman wutar da wani tsauni ke yi.
Rahotanni sun ce tsaunin Agung, da ke da nisan kilomita 75 daga wurin shakatawar Kuta, ya fara tumbatsa ne tun a watan Agusta da ya gabata, kuma rabonsa da yin haka tun shekarar 1963.
Kakakin ma’aikatar agajin gaggawa Sutopo Nugroho yace akwai alamu mai karfi dake nuna cewar za a samu aman wutar, wanda kuma shi ne dalilin da ya sa aka kwashe mazauna yankin zuwa wasu sansanoni domin kare lafiyar su.
Akalla mutane dubu daya ne suka rasa rayukansu sakamakon aman wuta da kuma narkakken dutse da tsaunin na Agung ya yi a shekarar 1963.