Connect with us

KASASHEN WAJE

Indonesia Ta Ceto Wasu ‘Yan kabilar Rohingya A Cikin Teku

Published

on

Hukumomin Indonesia sun ce sun ceto akalla ‘yan kabilar Rohingya 100 da suka fito daga Myanmar a cikin tekun dake kusa da tsibirin Sumatra, wadanda suka hada da yara 30 daga cikin su.

Shugaban hukumar tsaron teku a yankin Aceh, Muhammad Nasir ya ce an gano wadannan mutanen ne a cikin wani kwale-kwale mara inganci suna yawo a saman ruwa, kafin masu kamun kifi su gano su.

Nasir ya ce mutanen sun kwashe kwanaki a cikin teku ba tare da abinci da ruwan sha ba.

‘Yan kabilar Rohingya dake fuskantar mawuyacin hali a Myanmar na barin kasar zuwa kasashen Malaysia ko Indonesia domin samun mafaka, yayin da dama daga cikin su kan mutu a teku.

Shugaban hukumar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International a Indonesia Usman Hamid ya bukaci taimakawa wadannan baki da suka kunshi mata da yara wadanda ke kwashe kwanaki a cikin teku ba tare da abinci ba.
Advertisement

labarai