Muhammad Awwal Umar" />

INEC A Jihar Neja Ta Yaba Da Yadda Aka Fito A Zaben Da Ya Gabata

Hukumar zabe a jihar Neja ta bada tabbacin kara azama wajen ganin an samu ingantaccen zabe a jihar Neja. Shugaban hukumar, Farfesa Sam Egwu ne ya bayyana hakan a taron karawa juna ilimi da bada rahoto kan zabukan da suka gaba, wanda kungiyar ‘yan Jarida reshen ma’aikatar sadarwa ta shirya laraban makon a dakin taro na ma’aikatar lafiya.
Sam Egwu ya cigaba da cewar lallai hukumarsu tayi kokari matuka gaya amma an samu matsaloli wajen isar kayan zabe kan kari wanda a zaben gwamna da ‘yan majalisun dokoki hakan ba zai sake faruwa ba.
Zabe ba wai maganar hukumar zabe INEC ba ne, magana ce ta ‘yan kasa musamman dan ba su damar zabin shugabannin da suke ra’ayi wadanda za su jagorance a matakin shugabanci kan tsarin dimukuradiyyar.
Ina ganin tsarin dimukuradiyyar kasar nan an fara samun ci gaba ganin yadda jama’a suka fito dan yin zabe yadda ya kamata. Dan haka hukumar ta yaba da yadda ta ga masu sanya ido sun fito dan sanya idan yadda aka gudanar da zaben.
Farfesa Egwu ya bada tabbacin a wannan zaben mai zuwa hukumarsa ba za tai kasa a guiwa ba wajen ganin kayan zabe sun isa cibiyoyin zabe kan lokaci tare da tabbatar da an bi ka’idar da aka ajiye dan samun zabe mai tsafta kuma ya zama amintacce musamman wajen ganin kayan zaben sun isa kan kari.
Hukumar ta yabawa al’ummar Neja da suka fito suka jefa kuri’arsu wanda yasa jihar ta zama sahun gaba wajen samun zabe mai tsafta cikin kwanciyar hankali ba tare da samun hargitsi ba.
Shugaban ya karyata rahotanni da ake yadawa cewar hukumarsu ta baiwa jam’iyyun siyasa katin zaben da ba a riga an karba a hannunta ba, yace dukkanin katin zaben da ba a karba suna ma’ajiyar hukumar da ke reshen babban bankin Najeriya da ke Minna. Farfesa Egwu ya ce, bangaren tsaro jami’an tsaro sun taka rawar gani, domin ba zasu iya aikin da suka yi ba a yanzu, ya ce, ba a baiwa jami’an ‘yan sanda damar rike makami ba, suma sojoji da ke yawo da makamai a lokacin zabe ba sa kusantar runfunar zabe suna kan hanya suna ayyukansu na yau da kullun da suka saba. Ina mai jawo hankalin masu zabe da su zama masu bin doka da oda kamar yadda aka sanar.
Taron wanda aka shirya karkashin jagorancin Isma’ila Saba Fabu wanda Muhammed Muhammed ya jagoranta ya batutuwa da dama da suka shafi kurakurai da matsalolin da aka samu a zaben da ya gabata. Shugabannin hukumomin sadarwa da suka kunshi radio da talabijin da jaridu sun tattauna kuma sun baiwa hukumar zaben shawarwari ta yadda za a kara samun inganci a zaben mai zuwa na gwamna da ‘yan majalisar dokokin jiha.
Babban sakatare a ma’aikatar sadarwa ta jiha, Malam Isah Bala Ibrahim ya yaba da yunkurin wannan kungiyar ta NUJ reshen ma’aikatar na fadakar da hukumar da kuma masu ruwa da tsaki dan samun zabe mai tsafta a jihar Neja.

Exit mobile version