Sabo Ahmad" />

INEC Ta Bayar Da Sanarwar Zaben 2019

A jiya Juma’a ce Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayar da sanawar tsare-tsarenta na gudanar da zaben shekata ta 2019. Hukumar ta lika sanarwar ce a ofishinta da ke Abuja.

Misis Ndidi Okafor, shugabar wayar da kan masu zabe kuma jami’ar hulda da jama’a a wata kungiya da ke da alaka da Hukumar ta INEC Abuja, ta bayyana wa majiyarmu cewa, fitar da sanarwar da ta yi, ta yi daidai da sashi na 30 na dokar zabe ta shekara ta 2010.

Kamar yadda sanarwar ta ce za a karbi fom din ‘yan takarar da aka zaba a matakin kasa da jiha tsakanin 17  da  24 ga watan Agusta.

Haka kuma za a karbi fom din Abuja tsakanin 3 zuwa 10 ga watan Satumba.

“Ranar karshe ta mika fom din da jam’iyyu za su yi ita ce za ta kasance tsakanin. 3 ga Disamba, na shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya sai kuma  jihohi su kuma 17 ga watan Disamba.

“Sai kuma na ‘ya takara daga Abuja zai fara ranar. 3 ga watan Nuwamba zuwa 10, ga Nuwamba, rana ta karshe ta dawo wa fom din ita ce ranar.14.

“Ranar 25 ga watan Okotoba INEC  za ta buga bayanai a kan dukkan ‘yan takara, sai kuma na jihohi ranar 9. Ga watan Nuwamba

Okafor ta ce INEC ta sanar da ranar 17 Nuwamba ra ta karshe ta janye wanda za a maye gurbin wanda ya janye da wani dan takarar shugaban kasa ko dan majalisar tarayya sai kuma 1 ga Disamba ga gwamnoni da ‘yan majalisar jiha.

Ranar 2 janairu, 2019  za ta buga sanarwar zabe kuma 7 Janairu  2019 za a fitar da rajistar masu jefa kuri’a, wanda kuma za a fara da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya ranar 16 Fabarairu .

Exit mobile version