INEC Ta Bukaci Majalisar Tarayya Ta Maida Guraben Zabe Zuwa Rumfunan Zabe

Hukumar Zabe

Daga Nasir S. Gwangwazo, Abuja

 

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi kira ga Majalisar Tarayya da ta amince mata ta mayar da kananan guraben kada kuri’a da ke fadin kasar nan zuwa cikakkun rumfunan zabe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya yi wannan rokon a lokacin da ya gabatar da bayani kan yadda za a sama wa masu zabe rumfunan kada zabe (wato Pulling Units, PUs) a Nijeriya, a gaban Cikakken Kwamitin Majalisar Tarayya kan Hukumar Zabe da Al’amuran Zabe, a ranar Talata a Abuja.

Ya ce wasu daga cikin guraben kada kuri’ar idan aka maida su rumfunan zabe, za a kuma dauke su zuwa wuraren da aka fi bukatar su.

Haka kuma Yakubu ya yi kira ga ‘yan majalisar da masu ruwa da tsaki cikin lamarin da su taimaka su cire batutuwan siyasa daga cikin manufar hukumar, ya na mai cewa al’amarin ya shafi dukkan sassan kasar nan.

Ya ce samun wurin jefa kuri’a ga mutanen kasar nan ya shiga mugun yanayi a yanzu domin kuwa rumfunan zabe da ake da su a yau guda 119,973 tsohuwar Hukumar Zabe ta Nijeriya (NECON) ita ce ta samar da su shekaru 25 da su ka gabata.

Ya yi nuni da cewa a wancan lokaci an kiyasta cewa rumfunan zaben da ake da su yanzu za su yi wa masu zabe miliyan 50 da su ka yi rajista aiki ne, to amma sun karu zuwa sama da mutum miliyan 84 a cikin 2019 kuma ana sa ran za su karu kafin manyan zabubbukan da ke tafe.

Yakubu ya ce ban da karancin da rumfunan zaben su ka yi a yanzu, akwai kuma rashin dacewar su ga masu zabe, musamman ganin ana cikin yanayin annobar korona yanzu.

Ya kara da cewa ita ma Hukumar Zabe ta na shan wahala wajen gudanar da zabe cikin adalci da bin doka da oda a wadannan rumfunan.

Shugaban hukumar ya ce INEC ta sha yin kokarin magance matsalar a baya amma ‘yan Nijeriya ba su fahimtar manufar ta saboda rashin wayar masu da kai kuma da yake ana daukar matakan ne a daidai lokacin da zabe ya karato.

A cewar Yakubu, wasu daga cikin matakan da hukumar ta dauka don magance matsalar sun hada da kirkiro kananan wuraren zabe a cikin 2007, da guraben kada kuri’a a cikin 2011 da kuma unguwannin guraben zabe a Yankin Birnin Tarayya a cikin 2016.

Ya ce hukumar ta yi amanna da cewar idan aka maida kananan guraben zabe da ake ta amfani da su tun cikin 2011 zuwa rumfunan zabe tare da sauya wa wasun su matsuguni zuwa inda ya dace, to yawancin kalubalen da masu zabe da ita kan ta hukumar su ke fuskanta za su kau.

Yakubu ya ce ban da fara aiki da wuri kan batun da hukumar ta yi a yanzu, haka kuma hukumar ta yanke shawarar ta yi aiki kafada da kafada da wadanda ke da ruwa da tsaki cikin lamarin don magance wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.

Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu har hukumar ta samu sama da bukatu 9,000 daga unguwanni da daidaikun mutane a fadin kasar nan na a kirkiro masu rumfunan zabe.

“Mun samu kiraye-kiraye guda 5,747 a cikin Oktoba 2020 na mu kafa sababbin rumfunan zabe. Ba hukumar mu ba ce ta fada wa mutane cewa su rubuto bukatar su ta a kirkiro masu rumfunan zabe ko wani abu makamancin hakan.

“Ya zuwa makon jiya, 23 ga Fabrairu, yawan bukatun ya karu zuwa 9,092, wanda ya nuna karuwar 4,300 a cikin watanni hudu kuma har yanzu yawan ya na ci gaba da karuwa,” inji shi.

Ya bada tabbacin cewa idan aka maida kananan guraben zaben zuwa rumfunan zabe, hukumar za ta yi la’akari da yawan masu zabe da su ka yi rajista a kowace rumfar zabe da kuma tazarar da ke tsakani, don tabbatar da cewa an yi adalci kuma an magance matsalar sosai.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya yi alkawarin cewa Majalisar Tarayya za ta mara wa INEC baya wajen samar da yanayin zabe mafi nagarta ga ‘yan Nijeriya ta hanyar kirkiro karin rumfunan zabe.

Lawan ya ce, “Ina so in tabbatar wa da Shugaban Hukumar Zabe da ma ‘yan Nijeriya cewa Majalisar Tarayya za ta ba INEC cikakken goyon baya, ba tare da inda-inda ba, don tabbatar da mun samar da yanayin zabe mafi inganci ga mutanen kasar mu.

“Za mu yi dukkan abin da ya dace, domin manufar mulkin dimokiradiyya ita ce a ba kowa dama kuma zabe shi ne kusan abin da ya fi komai muhimmanci.”

Yakubu ya samu rakiyar kwamishinonin kasa da wasu daga cikin jami’an gudanarwa na hukumar zuwa majalisar.

Exit mobile version