Bello Hamza" />

INEC Ta Ce, PDP Ce Ta Lashe Zabukan Zamfara: Ta Ayyana Matawallen Maradun A Matsayin Zababben Gwamna

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar Alhaji Bello Matawalle dan takarar kujerar Gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara a zaben 2019 a matsayin zababen gwamnan jihar Zamfara.
INEC ta bayyana haka ne a taron manema labarai data kira jiya Asabar, inda shugaban hukumar Fafersa Mahmood Yakubu ya kara da cewa, hukumar INEC za ta gabatar wad a ‘yan takarar jam’iyyar PDP takardar shaidar lashe zabe a gobe Litinin.
A ranar jumma’a ne hukumar ta INEC ta bayyana cewa, za ta shawara a kan hukuncin da kotun koli ta yanke inda ta yi watsi da dukkan kuri’ar da jam’iyyar APC mai mulki ta samu a zaben da aka gudanar a 2019 a jihar.
“Hukumar za ta yi taro a gobe Asabar 25 ga watan Mayu 2019 don tattaunawa da yanke hukuncin a kan hukuncin kotun kolin yayin da za a sanar da jama’a halin da ake ciki a ranar Litinin 27 ga watan May 2019,” a sanarwa da Festus Okoye Kwamishinan watsa labarai da wayar da kan masu jefa kuri’a ya bayar tunda farko.
Amma a jiya Asabar hukumar ta INEC ta kira taron manema labarai inda ta sanar da ‘yan takarar jami’iyyar PDP a matsayin wadanda suka lashe zabe, kuma za a basu takardar shaidar lashe zaben a gobe Litinin.

Exit mobile version