INEC Ta Fitar Da Jadawalin Zabukan 2023

Daga Muhammad Awwal Umar Minna,

Hukumar zabe ta kasa ta bayyana cewar babban zaben shekarar 2023 zai kasance ranar 18 ga watan Fabrairu ga shugaban kasa da mataimakinsa, sai na ‘yan majalisar wakilai da dattijai da na sanatoci duk a rana daya.

Sanarwar ta cigaba da cewar zaben gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jahohi kuma zai kasance ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2023. Wadanda suka samu nasara kuma za a rantsar da su ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Exit mobile version