INEC Ta Janye Rumfunan Zabe 749 Daga Wuraren Ibada

Zaben Dan Majalisa

Daga Sulaiman Ibrahim

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ta cire rumfunan zabe 749 daga wuraren da ba su dace ba a duk fadin kasar nan.

Masu sa ido kan rumfunan zabe na hukumar sun ce an cire tara daga cikin wuraren bauta tare da wasu da yawa daga gidajen addini, da gidajen sarauta, da gidaje masu zaman kansu.

Da yake magana a Abuja a wani taron ganawa da Kwamishinonin Zabe (RECs), shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce daga cibiyoyin kada kuri’u na farko 119,973, yanzu al’ummar kasar nan na da rumfunan zabe 176, 846 cikakku.

Zamu kawo cikakkun bayanai daga baya…

Exit mobile version