Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Hukumar zaɓ e mai zaman kanta ta wato INEC reshen jihar Bauchi ta nuna matuƙar damuwarta, akan yadda ‘yan siyasa suka baje tare da maida, fadar jihar ta Bauchi da hotonan, allunan tallar ‘yan takarkaru duk da lokacin buga gangan siyasa bai yi ba, a cewar Hukumar wannan sam bai dace ba, a bisa haka ta himmatu domin ɗaukar matakin da ya dace dangane da al’amarin.
Kwamishinan Hukumar zaɓ en na jihar Bauchi Alhaji Ibrahim Abdullahi ya shaida hakan a lokacin da tawagar wasu jiga-jigan ‘yan siyasa suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar larabar nan da ta gabata.
Alhaji Abdullahi Ibrahim ya ce, irin waɗannan halaye na baje kolin posta-posta a cikin garin ba fa, za su zura ido su bari, hakan na cigaba, idan aka yi la’akari da cewar, Hukumar bata bada damar fara gangamin kamfen na neman kujera, ga kowa ba zuwa yanzu. Ya tunatar da ‘yan siyasa da masu yi masu bangar siyasa kan wannan inda ya ce Hukumar ta INEC tana fa da tsare-tsaren da take tafiya a kai, a bisa haka ya tunatar da ‘yan siyasa da sauran lokaci.
Tun da ya fara na shi jawabin, Alhaji Uba Ahmad Nana Shugaban jam’iyya mai mulki a jihar ya yi kira ne ga Hukumar ta INEC da ta tabbatar da samar da daidai gabanin, da kuma bayan gudanar da zaɓ e, ya ce hakan zai bada dama a samu gudanar da zaɓ en cikin tsafta a ciki da wajen jihar ta Bauchi.
A wani labarin kuma, Kwamishinan Hukumar INEC ta Jihar Bauchi Alhaji Ibrahim Abdullahi ya yi kira ga sarakuna su shiga, a dama da su wajen yin rijistar katin zaɓ e, tare da faɗakar da jama’a kan yin rijistar wanda zai ba jama’a damar zaɓ an, wanda suke so. kwamishinan wanda ya bayyana hakan a sa’ilin da ya kai ziyara masarautar Bauchi a cikin makon nan.
Kwamishinan ya ce masarautun gargajiya suna da muhimmniyar rawar da suke iya takawa wajen samar da tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati ya kai ga gaci, a bisa tasirin da suke da shi, a cikin al’umma tun daga cikin Birane da kuma Yankunan karkara “Na zo yau na roƙi Sarki ya taimaka wajen samun nasarar abin da muka sa a gaba na yin rijistar katin zaɓ e, na waɗanda suka cancanta”.
Kwamishinan INEC ya kuma nuna damuwarsa a sakamakon yadda masu ruwa da tsaki suka gaza faɗakar da mutanensu, kan muhimmancin yankar katin da zai basu zarafin shiga a dama da su, a lokacin da aka fara gudanar da zaɓ e da ke tafe. Daga bisani ne kuma ya sha alwashin jagorantar gudanar da tsaftataccen zaɓ e, a cikin jihar ta Bauchi a zaɓ en shekara ta 2019 da muke fuskanta.
A nashi jawabin, mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji (Dr) Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayyana aniyar masu riƙe da sarautun gargajiya da cewar, za su bada himma wajen ganin an samu nasarar gudanar da aikin zaɓ e cikin tsafta, tare da ƙoƙarin da za su yi wajen faɗakar da jama’a kan yin katin na zaɓ e.