INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

INEC Ta Shirya Gudanar Da Zaben Cike Gurbi A Jihar Kano

bySadiq
2 years ago
INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa(INEC) a Jihar Kano ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomin Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garin Malam da Rimin Gado/Tofa na majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a cikin watan Fabrairu. 

Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango ne, ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki a hedikwatar hukumar da ke Kano a ranar Talata.

  • Da Dumi-dumi: Kotun Koli Ta Tanadi Ranar Yanke Hukunci Kan Shari’ar Kujerar Gwamnan Filato
  • Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Emefiele N100m Kan Tsare Shi Ba Bisa Ka’ida Ba. 

“Mun shirya tsaf domin gudanar da zaben tare da kwararru wanda jami’an zabe a shirye suke su gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi shida na jihar.

“Za mu gudanar da zabe a rumfunan zabe 66 a fadin kananan hukumomin shida.

“Duk mutumin da ba shi da katin zabe ba zai yi zabe a kananan hukumomin ba,” in ji shi.

Ya ce tuni hukumar ta tura wasu muhimman kayayyaki ga daukacin kananan hukumomin da abin ya shafa.

Zango ya bayyana cewa za a yi amfani da na’urar BVAS a yayin sake gudanar da zaben da nufin tabbatar da sahihin zabe.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar kan gudanar da zaben cike gurbin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya samar da tsaro a dukkan harkokin zabe a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Gumel wanda ya samu wakilcin CSP Hamma Abdullahi, ya ce ‘yan sanda za su tura jami’an tsaro kowace rumfar zabe domin bai wa mazauna kananan hukumomin shida.

Ya gargadi shugabannin jam’iyyun siyasa da za su shiga zaben da su ja hankalin magoya bayansu da su guji tada tarzoma.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Next Post
Sin

Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa A Harkokin Duniya

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version