INEC Ta Shirya Tsaf Domin Fara Rijistar Masu Zabe – Yakubu

INEC

Daga Yusuf Shuaibu,

Kasa da shekaru biyu da a gudanar da babban zaben shekarar 2023, a ranar Litinin ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa, ta kammala aikin samar da karin mazabu a cikin kasar nan. Saboda haka, hukumar ta ce za ta wallafa sunayan sababbin mazabu a mako mai zuwa. Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana hakan lokacin da ake amsar sababbin naurorin kashe gobara daga wajen hukumar kashe gobara ta kasa.

Rahotannin sun bayyana cewa hukumar ta samar da sababbin mazabun ne saboda a magance matsallin cinkoso da ake samu lokacin gudanar da zabe a cikin kasar nan.

“Muna tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hukumar zabe ta shirya tsaf wajen gudanar da rijistar masu zabe bayan ta kammala gabatar da sababbin mazabu a cikin kasar nan. Ina farin cikin bayar da rahoton kammala wannan gagarumar aiki da aka kwashe shekara 25 ana kokarin yi,” in ji Yakubu.

A cewarsa, cikakken bayanin wuraren cibiyoyin rijistar za a gabatar da su a intanet bayan an kammala tattaunawa da masu ruwa da tsaki a mako mai zuwa.

Da yake jawabi a kan girke na’urar kashe gobarar a hukumar, Yakubu ya bayyana cewa wata alama ce a dai-dai lokacin da hukumar ta fuskanci farmaki guda 42 a ofishoshinta da ke fadin kasar nan.

Ya ce, “idan za a iya tunawa a kan wannan lamari, hukumar ta gudanar da taron gaggawa da tare da hadakar kwamitin tattaunawa wadanda suka hada da jami’an tsaro a makon da ta gaba ta.”

 

Exit mobile version