Connect with us

LABARAI

INEC Ta Yi Rijistar Mutum Miliyan 1. 3 A Jihar Yobe

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), a jihar Yobe, ta bayyana cewa ta yi wa mutane miliyan daya da digo uku (1. 3m) rijistar katin zabe a jihar. Inda yanzu haka kuma aikin rijistar katin masu jefa kuri’ar ke ci gaba da gudana.
Kwamishinan INEC a jihar Yobe, Alhaji Ahmadu Makama ne ya bayyana hakan a sa’ilin da yake zanta wa da manema labarai a ofishin sa dake Damaturu, babban birnin jihar. Inda ya ce INEC ta na kokari wajen tabbatar da sai wadanda shekarun su suka kai ne kadai za a yi wa rijistar.
Bugu da kari kuma, ya shaidar da cewa hukumar INEC ta dauki matakan dakile dabi’ar maimaita yin rijistar katin sau biyu da wasu ke yi.
Makama ya yi karin haske da cewa, daga watan Aprilu zuwa na Disambar shekarar 2017, sun yiwa mutum 159,221 rijistar katin ta din-din-din a jihar, wanda bayan tantancewa ne mutane 90,354 ne suka yi saura; a kokarin su na maimaita yin rijistar.
A bayanin nashi ya ce, a tsakanin watan Aprilu zuwa na Disambar shekarar da ta wuce, hukumar su ta kawo katin zaben ta din-din-din a jihar har guda 69,052, wanda kuma daga cikin wannan adadin sun raba wa jama’a katin har 22,474.
Har wa yau kuma, ya ce, a cikin wancan adadin akwai katin zaben 33,000 da masu shi ba su zo sun karba ba. Ya ce, mutane yan kadan ne ke zuwa hukumar INEC din neman canjin gari, wanda ya bayyana cewa mutum 173 kacal suka mika bukatar canjin muhalli, domin jefa kuri’ar.
Alhaji Makama ya ankarar da cewar, tun tuni hukumar ta fara aiwatar da shirye-shiryen yadda za ta tunkari babban zabe mai zuwa, na shekarar 2019.
“Yanzu haka mun fara gudanar da tattauna wa da kungiyar direbobin motocin sufuri ta kasa (NURTW), dangane da yadda zamu tsara aikin rarraba kayan zabe da jami’an mu, zuwa kowanne lungu da sako”.
Hukumar INEC ta bukaci samun hadin kai da goyon bayan jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro tare da yan jaridu da sauran jama’a wajen ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, a lokacin gudanar da zaben a jihar Yobe.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: