Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa, za ta sake zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya a Jihar Zamfara yau Laraba, bayan da hukumar ta soke zaben sakamakon aringizon kuri’u da a ka yi da kuma satar akwatinan zaben.
Sai dai kuma tsohon Gwamnan jihar ta Zamfara, Hon. Abdul’aziz Yari, ya yi barazanar cewa, jam’iyyar APC ba za ta shiga zaben da za a yi a yau din ba, wanda hukumar ta soke idan har ba a tabbatar da tsaro ba.
Yari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ya zantawa da manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na APC da ta gudanar a gidansa da ke Talata Mafara.
Tsohon Gwamnan ya zargi Gwamna Bello Mohammed Matawalle na Jihar Zamfara da manyan ma’aikatan gwamnatin jihar da hada baki da wasu jami’an tsaro, don murde zaben ta hanyar goyon bayan Jamiyyarsa ta PDP.
Yari ya kuma zargi kwamishinan kudi, Alhaji Rabiu Garba, da na Kananan Hukumomi da Cigaban Al’umma, Alhaji Yahaya Chado, da Kwamishinan Aikin Gona, Dr. Yarkofoji, da kwace akwatin zabe a lokacin zaben, wanda a ka bayyana a matsayin wanda bai kammala ba.
Tsohon gwamnan ya ce, idan har jami’an tsaro ba su tsara abubuwan da za su tabbatar da tsaron wakilan APC da magoya bayansu ba, jam’iyyar ba za ta jefa rayukan wakilanata da magoya bayanta cikin hadari ba a zaben na Laraba.
“Abinda ya faru a ranar Asabar ba za a iya bayyana shi a matsayin zabe ba, amma abin kunya abin takaici ne matuka cewa jami’an tsaro, wadanda ya kamata su tabbatar an gudanar da zaben cikin lumana, su ne wadanda ke ba da goyon baya da goyon bayan manyan ma’aikatan gwamnati da wakilan PDP wajen kwace akwatunan zabe.
“Don haka idan jami’an tsaro ba su dauki gagarumin mataki ba, don kauce wa abinda ya faru a ranar Asabar ba, to za mu janye ba za mu shiga zaben ba,” in ji Yari.
Haka kazalika, Jamiyyar PDP reshen jihar Zamfara ta nuna kaduwarta kan kalaman da jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ibrahim Magawata, ya yi yayin a zaben maye gurbin da ya gabata a jihar.
“Kuma mu ba mu gamsu ba da Farfesa Magawata a kan jagorancin gabatar da zaben a gobe laraba da za’a gabatar,” in ji ta.
Da ya ke jawabi a taron manema labarai a Gusau, Shugaban Kwamitin PDP kan zaben Bakura, Sanata Lawal Hassan Dan’Iya, ya koka kan cewa jami’in tattara sakamakon ya nuna bangaranci. A lokacin bayanin jami’in tattara sakamakon zaben na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a zaben maye gurbin ranar Asabar din da ta gabata a Mazabar Bakura ta jihar Zamfara, Farfesa Ibrahim Magatawa ya nuna bangaranci wajan fadi sakamakon zaben,” in ji Dan’Iya.
“Kuma tsafin ‘Yan majalusun tarayya irin su Sani Jaji da Abudulmalik Zanna da Kwamishinonin tsohon Gwamna Yari, sun taka rawa wajan ganin sun yi magudin zabe da amfanin da ’yan ta’adda, don kawo wa zaben cikas,” in ji Sanata Dan’Iya.
“Duk mai kaunar dimukradiyya ya yi Allah-wadai da dabi’un APC wajen daukar ’yan daba, musamman daga yankin Zuru na Jihar Kebbi ta su ka kawo su a mazabar, Dakko da Damri wadanda da gangan suka zo ba tare da son rai ba su ka tayar da rikici a lokacin zaben.
“Babban damuwarmu shi ne yadda a ka yi amfani da jami’ai cikin kaki, don kare munanan ayyukan masu karya doka. Mu na matukar damuwa yadda wasu jami’an tsaro su ka kauda kai daga ayyukan ‘yan baranda su ka cigaba da bayar da kariya ga su ‘yan ta’adan,” in ji shi.
Sanata Daniya ya ce duk da soke zabe a rumfunan zabe 14, PDP ta lashe zaben gabadaya ba za mu karaya ba a zaben gobe kuma gaskiya za ta yi halin da da yardar Allah APC, sai ta kunyata a zaben.