Daga Abubakar Abba, Kaduna
Hukumar Zabe ta kasa INEC da ke jihar Kaduna ta bayyana cewa a ranar Litinin 21 ga watan nan na Augusta ne za ta rufe yin rijista a karin cibiyoyin nan takwas da ta bude a Ladduga, Katugal, Gonin Gora, Kwarbai ‘B’,Tudun Nufawa, Gidan Waya, Unguwar Rimi da kuma gundumar Rigasa.
Bayanin hakan yana kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Sashen mulki na Hukumar, Nick Dazang ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai a Kaduna cikin makon nan.
Sai dai, Nick ya ce za a ci gaba da yin rijistar a ofishoshin Hukumar dake Kananan Hukumomi 23 da ke jihar. Don haka ta shawarci wadanda suka kai munzalin jefa kuri’a da su gaggauta zuwa cibiyoyin da aka bude kafin a rufe yin rijistar.