Abba Ibrahim Wada" />

Infantino Ya Sake Lashe Zaben Shugaban FIFA Karo Na Biyu

An sake zaben Gianni Infantino a matsayin shugaban hukumar  kwallon  kafa ta duniya Fifa a karo na biyu a jere a zaben da akayi ba tare da dan takara ba wanda kuma hakan yabashi damar sake shugabantar hukumar nan da wasu shekaru hudun masu zuwa.

Infantino, mai shekara 49 a duniya ya sake tsayawa neman cigaba da shugabantar hukumar ne ba tare da wani dan takara ba kuma aka kada  kuri’a kamar yadda yake a al’ada a babban taron hukumar karo na 69 wanda akayi a shedikwatar hukumar dake Switzerland.

Bayan kammala zaben Infantino ya godewa wadanda suka kada  kuri’ar inda kuma ya bayyana cewa yana neman goyon bayan duk wani wanda yake mamba ne a hukumar kuma bazai tsaya ba wajen ganin ya cigaba da kawowa hukumar cigaba.

“Ina sake godiya ga irin damar da aka sake bani domin sake shugaban cin wannan hukuma kuma zan tabbatar na cigaba da kawo cigaba musamman wajen ganin cigaba  kwallon  kafa ta matasa da kuma mata” in ji Infantino, dan  kasar Italiya

Ya cigaba da cewa “Tun lokacin da yazama shugaban hukumar shekaru hudu da suka gabata yayi maganin maganar cin hanci da rashawa sannan kuma ya kawo  karshen duk wani abu daya damu hukumar”

Infantino ya zama shugaban hukumar  kwallon  kafa ta duniya ne a shekara ta 2015 bayan da rikicin cin hanci da rashawa ya mamaye hukumar a  kar kashin tsohon shugaban hukumar, Sepp Blatter.

Exit mobile version