Yusuf Shuaibu" />

Inganta Ma’adanai Zai Bunkasa Tattalin Arziki – Minista

Bangaren Ma’adanai

Ministan ma’adanai da bunkasa karafa, Olamilekan Adegbite ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana kokarin bayar da goyan baya ga kamfanonin ma’adanai, domin samun samar bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga ’yan Nijeriya.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da ya je rangadi a aikin kamfanin hakar zinari da ke yankin Iperindo cikiin Jihar Osun.

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta karkashin ma’aikatarsa za ta samar da harkokin kasuwanci  mai kyau domin karfafa fannin.

Wasu daga cikin yanayin  harkokin kasuwancin mai kyau sun hada da yafe harajin shigowa da kayayyakin aiki da shigowa da injina na hakar ma’adanai da yafe harajin samar da kayayayaki har na tsawan shekara biyar a cikin harkokin kasuwancin.

Sauran sun hada saukaka zirga-zirgan kudade da amincewa da samun saukin yin canji da barin su zuba jari na kashi 95 da cire musu harajin wajen zama da hannan ta musu mallakar kayayyakin ma’adanai kashi dari bisa dari.

Ya ce, “muna bukatar mayar da Nijeriya babban wajen samar da zinari a yankin Afirka, wannan ne ya sa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da goyan bayanta ga fannin ma’adanai, domin tabbatar da bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage dogaro da mai.”

Tun da farko dai, shugaban gudanar da aikin , Segun Lawson ya bayyana cewa, duk da matsalolin da ake fuskanta sakamakon cutar Korona, kamfanin zai fara aiki ne a wata biyun wannan shekara.

Haka kuma, ya bayyana cewa kamfanin yana tsammanin samar da zinari mai dauyin 80,000 a kowacce shekara a lokacin da yake hakar ma’adanai. Lawson ya kara da cewa, wannan kamfani zai samar wa mutane 500 aikin yi kai tsaye da kuma samar wa mutum 1100 ayyukan yi wanda ba na kai tsaye ba.

Ya ce, duk da irin matsalolin da suke fuskanta sakamakon cutar Korona, ba zai su yi kasa a gwiwa ba wajen samun ingantattun kayayyakin ginin da ake bukata a duniya.

Ya kuma jaddada cewa, a wannan yakin da kamfanin yake ya bayar da tallafin karatu kyauta a fannin sakandare da manyan makarantu wanda da ya kashe miliyoyin nairori.

Exit mobile version