Inganta Makarantun Allo: UNICEF Da Hukumar Tsangayu Sun Hada Hannu A Kano

UNICEF

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Hukumar Makarantun Allo da Islamiyyu da hadin guiwar Hukumar UNICEF sun kaddamar da kidayar makarantu da aka shigar tsarin ilimin zamani da wadanda ba’a shigar ba 13,696 da aka gudanar a fadin Jihar Kano, domin fara shirin aiwatar da  Ilimi kyauta kuma wajibi ga kowa da Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar.

Da yake gabatar da jawabinsa a wurin taron da aka gudanar cikin makon day a gabata, kwamishinan Ma’aikatar Ilimi na Jihar Kano, Wanda  Daraktan sashen ilimin addini (IED) Malam Dayyabu Ahmad Mustapha ya wakilta cewa ya yi, adadin makarantun da aka shigar cikin wannan tsari sun kai 119, inda Karamar Hukumar Bichi keda adadi makarantu 39. Ya yinda da sauran wadanda ke kan hanyar shiga cikin shirin ya kai adadin 13,319 wadda Gezawa ke kan gaba da adadin cibiyoyi 978, sai Karamar Hukumar Garko wacce keda mafi kantar cibiyoyi 53.

Saboda haka, Gwamnatin Jihar Kano da abokan hada guiwarta suka ga ya zama wajibi a cike gibin dake tsakanin makarantun da ke cikin shirin da sauran wadanda har yanzu basu shiga cikin shirin ba. Ya jaddada bukatar samar da wannan kididdiga a kowace shekara uku domin zama shaidar tsare tsaren Shirin.

Da yake gabatar da jawabin maraba Shugaban Hukumar Makarantun Allo da Islamiyya na Jihar Kano, Gwani Yahuza Gwani Danzarga  ya bayyana godiyarsa ga Hukumar UNICEF bisa gudunmawar kudi da take baiwa Gwamnatin Jihar Kano domin samar da ingantattun bayanai kan tsarin shigar da makarantun Allo da Islamiyya a Jihar Kano, wanda zai taimakawa Gwamnatin Jihar Kano samun cikakken matsayi da kulawa ga ilimin Alkur’ani. Ya kara da cewa samun bayanai zai inganta damar samun ingantaccen ilimin bai daya a Jihar Kano.

Da yake gabatar da jawabinsa jami’in Hukumar UNICEF Mr. Saka Adebayo Ibrahim cewa ya yi, ingantattun bayanai, tsari, cigaban Shirin da sabbin dabaru a fannin Ilimi zasu kara inganta Shirin, yace  muhimmancin bayanai kan tsarin Ilimi, shirye shiryen hadawa da daukar mataki ba zai Kididdugu ba. Kamar yadda Jami’in yada labaran Hukumar Makarantun Allo da Islamiyya Aminu Ahmad Turaki ya Shaidawa LEADERSHIP A Yau.

 

Exit mobile version