Connect with us

LABARAI

Inganta Makarantun Allo Ya Dace A YI Ba Rufe Su Ba – Mai ’Yan Makaranta

Published

on

Tun daga lokacin da wasu gwamnonin arewa suka kaddamar da shirin rufe makarantun Allo tare da mayar da daliban makarantun zuwa jihohinsu na asali, al’umma da dama suke ci gaba da gwamnonin shawarwarin matakan da suka kamata su dauka da haifar da da mai ido ga daliban da al’amarin ya shafa da kuma addinin musulunci baki daya.

Baya ga wasu al’umma da suke ba gwamnonin shawarwari, majalisar tarayya ma, ta umurci gwamnonin da suka fara aiwatar da wannan shiri, da su dakata, amma zuwa hada wannan labara, daya daga cikin jihohin ba su saurai shawarwarin  da ake ba su ba, kuma ba su saurari umurnin da majalisar tarayya ta ba su ba.

Kan wannan mataki da gwamnonin suka dauka, Shekh Alaramma Tanimu Mai ‘Yan Makaranta da ke gundumar Dutsen Abba a karamar hukumar Zariya, ya shiga sahun wadanda ke bayar da wannan shawarwari ga gwamnonin Arewa da su toshe kunnuwarsu daga karba ko kuma sauranan shawarwarin da ake ba su na dakatar da mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali, kamar yadda majalisar tarayyar Nijeriya ta ba su.

Alaramma Malam Tanimu ya ci gaba da cewar, ya dace gwamnonin su saurari shawarwarin da ae ba su, domin, a cewarsa, in har suka ci gaba da aiwatar da wannan tsari, a kwai illoli ma su yawa da za su taso ga yaran da matsalar ta shafa, musamman na yadda mafiya yawan almajiran da ake mayar da su garuruwansu, a garurun da aka mayar da su babu makarantun da za su ci gaba da neman ilimin da suka fara, kuma babu makarantun zamani da gwamnonin suka fi son yaran su yi.

A kan haka ne masanin addinin musuluncin ya ce, mataki na farko da ya dace gwamnonin su dauka shi ne, su nemi wadanda ke da makarantun, su nemi shawarwarin da za su bi domin inganta makarantun, kamar yin gine-gine da kuma ba malaman kayayyakin abincin da za su ciyar da daliban da suke da shi, wannan su ne mataki na farko, a cewarsa, da ya dace, gwamnonin su dauka, in da gaske ne sun a kishin makomar rayuwar yaran da suke ganin mayar da su garuruwansu, shi ne zai sa su zama mutane nagari a gobe.

Sauran matakan da Alaramma Malam Tanimu ya ce ya kamata gwamnonin su yi shi ne, neman malaman da suke da makarantun, su ji matsalolinsu, su tabbatar da malaman ne, ko ‘yan gado na cewar, su ma iyayensu sun mallaki makarantun Allo? Idan an dauki wadannan shawarwari daya bayan daya, kuma aka aiwatar dad a kyakkyawar manufa, wannan matsala da ake ganin rayuwa ce mara kyau ga yaran zai zama ma fi alheri, maimakon daukansu zuwa jihohinsu ko kuma garuruwansu da aka sa wa gaba.

A game da yunkurin da gwamnatin tarayya ta yi da hadin gwiwa da majalisar dunkin duniya na cusa ilimin zamani a cikin makarantun allo kuwa, Sjekh Mai ‘Yan makaranta ya nuna cewar, wannan tsari in har an aiwatar da shi, ba zai haifar da da mai ido ga yaran ba, a cewarsa, tsari ne da wasu a wasu kasashe suka yi, domin aiwatar da wasu manufofinsu na boye, ba ciyar da addinin musulunci gaba ko kuma tallafa wa rayuwar matasan da aka tsari tsarin dominsu ba.

Kamar yadda Shehin malamin ya ce, ma su aiwatar da tsarin ba mutane ne da suka san wannan bangare na makarantun Allo ba , kuma babban abin da suka sa wa gaba shi ne aiwatar da tsarin da ma su fito-na-fito da Musulunci da kuma musulmi baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: