Connect with us

NOMA

Ingantaccen iri Ne Sirrin Samun Amfani Mai yawa

Published

on

Wannan wata tattaunawa ce da Sabo Ahmad Ya yi da Daraktan yankin Arewa-maso-yamma na hukumar samar da ingantaccen iri, a cibiyar Bincike ta wayar da kan manoma da bayar da dabarun noma ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru zariya, jim kadan bayan kamala gabatar da lacca a kan ingantaccen iri, yadda yake da kuma yadda ake samar das hi. Masu karatu ku biyo mu don karanta yadda tattaunawar ta kasance:
Ranka ya dade za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatu
To suna ma Malam Muhammad Hudu Uban Doma, Darakta na yanki na hukumar samar da iri na Arewa-maso-yamma, wanda ke da helkwata a Zariya.
Mene ne aikin wannan hukuma taku?
Wannan hukuma aikinta shi ne ta sa idanu ta tabbatar da manomi ya samu iri ingantacce, domin iri shi ne mataki na farko a noma, a duk lokacin da manomi bai samu iri ingantacce ba ko iri mai kyau ba to ya fadi. Duk sauran abin da za a sa, irin su taki da maganin kwari suna taimaka wa iri ne. Idan ka samu iri mai kyau to kashi hamsin na abin da za ka noma ya samu, saboda haka shi ya sa gwamnati ta tsare wannan domin kar a cuci manomi domin noman nan shi ne sana’anmu.
Yanzu ka gabatara da da kaitaccen bayani a kan iri, ko za ka gaya wa masu aratunmu, wannan bayani da ka yi?
To kasidar da na gabatar a wannan wuri na taron karawa wa masu ruwa da tsaki a kan harkar noma ilimi, wanda Africa Rice suka shirya. Shi ne mu sanar da su matakai da ake bi na noman iri a hukumance, domin noman iri ba wani abu ne da aka bar shi a bude kawai ba, gwamnati ta sa matakai na tsaro kuma ta sa hukumar da za ta lura da wannan, saboda haka wanda zai yi wannan aiki ya san menene ake bukata, domin me? Ya yi abin da manomi zai yi farin ciki da shi ba kuma ya kara mai asara ba, domin an tanaji hukunci na mutumin da zai sayar da iri ba mai kyau ba, ka ji na yi bayana mai yawa akan matakai da kuma laifuka. Duk mutumin da ya kawo iri mara kyau ya ba wani, to tara ne an kawo shi dubu dari shida da hamsin (650,000) zuwa miliyan guda (1,000,000), sannan kuma ana iya daure shi shekara biyar ko a hada mai duka, saboda haka muna fadakar da su su gane ba kasuwanci ne, ba kamar yadda aka gada ba, su gane wannan abin da zan yi ga hukunci a kaina. Kuma alherin da ke ciki Allah shi ya san yawansa, domin kana iya sayar da buhun masara ko buhun shinkafa ka samu dubu hamsin, ka ga wannan wani alheri ne.
Wadannan wadanne matakai ne a takaice?
Matakai na farko, na farko shi ne, duk mutumin da zai sai da iri sai ya yi rijista da hukuman da ake ce mata CSC da aka bata dama ta yi ma duk wani kamfani da za su yi a Nijeriya, su basu license, daya kenan, biyu, da wannan certificate din za ka yi rijista da mu, ka ga ka samu daman an baka iko ka yi kasuwanci a Nijeriya, to sai ka yi rijista da mu, kuma na fadi abubuwan da ake bukata na wannan rijista din, abubuwa ne da yawa sun kai wajen guda goma sha biyu, wanda zai bude kamfani ya nemi registration da mu sannan ya zama yana da kwararru wadanda za su yi wannan aikin iri din, ba noma ne gama gari ba, wannan noma ne a kimiyyance, saboda akwai abubuwan da ake so a gani kimiyyance, idan irin nan bai bada wadannan abubuwan ba, ba iri ba ne, na yi magana suna da yawa saboda me? Akwai matakai guda biyu, mataki na farko sai ya yi daidai da bukatun da ake so a fili, wanda muke ce Field Standard, in ya yi wannan, na biyu kuma sai an dauka an kai dakin gwaji ya bada abinda ake bukata a dakin gwaji shine Laboratory test sun yi satisfying wannan, nan mu aikinmu da na ce Third party guarantee muke badawa, kaman mune na uku, da mai yi, kamfani da wanda zai saya muna tsakiya ba cuta ba cutarwa ga kowanne a cikin su.
Wane sako kake da shi ga sauran manoma?
Yauwa, to abin da muke gaya wa manoma shi ne kamar yadda na ce maka iri shi ne matakin farko a aikin goma, saboda haka idan manomi zai saya iri mun sha gaya masu su rabu da wannan tsaffin iri da ake ajiyewa shekara arba’in, talatin baya. Yanayi ya canza, sabbin irin da aka kawo su yanzun don su yi maganin wannan yanayi da muke ciki ne, in an samu rashi ruwa in ka shuka abin ka an yi asara, amma yanzu akwai iri mai jure wa fari, akwai wurare wanda kuduji ko wuta-wuta saboda noman dawa da ake yi, da gero kowanne lokaci ya sa sun mamaye gonaki ba a iya nona masara, yanzu an samu masara wadda ke jure ma irin wadannan, an samo masara wanda za ta iya jure ma dan taki kadan kuma ta samu amfani mai yawa, to saboda haka asara ne gwamnati ba ta so manoma su yi, to saboda haka muna so su nemi wannan iri ingantattu an yi don su ne, akwai iri wanda aka yi shi mai sinadarin nama wanda za a iya ba yara ‘yan yaye wanda za su yi bulbul ba sai an sayi madara ko wani abu ba saboda matsalan kudi a karkara. In suna amfani da wannan masara yaro zai girma ya yi kuzari. Sannan akwai iri na masara da aka samo mai gyara ido wanda in mutum na da matsalan ido yana cin wannan masara, in Allah ya yarda zai dawo ya zauna lafiya, duk wannan gwanati ta sa kudi ta yi aiki domin su ne, saboda haka idan ba su zo sun yi amfani da shi ba to me ake yi?
Ta ya ya manomi zai gane ingantaccen iri?
Ingantaccen iri kamar yadda na gaya masu, mun yi kamfen na yi magana a rediyo in sun ji ni sun san wannan ci gaba ne, duk wanda zai sai iri na farko ya duba jakan irin akwai suna? Akwai nanbar waya na kamfanin? Akwai adireshi? Sannan ya duba cikin buhun zai ga kati guda biyu, akwai kati mai launin shudi, zai ga tambarin wannan hukuma namu sannan kuma zai ga katin kamfanin a wurin, idan ya samu wadannan abubuwa guda uku to duk matsalar da ya samu ya nufi ofis dinmu, bai da matsala, amma in bai da wadannan abubuwa ukun ya je wajen ‘yan damfara sun shafa kala ya saya ba wannan abubuwa ya saya to ya yi wa kansa asara. To abin da za su lura da shi ke nan.
Advertisement

labarai