Rabiu Ali Indabawa" />

Ingila Ba Ta DA Mafita Illa Ficewa Daga Tarayyar Turai Ko Ba Yarjejeniya – Johnson

A aranar Laraba Faraministan Britaniya Boris Johnson a ya kara matsa kaimi ga kungiyar tarayyar turai, tare da barazanr cewa, kasarsa na shirye ta fice daga kungiyar tarayyar turai ko da yarjejeniya kobabu, a ranar 31 ga watanan wata na Oktoba da muke ciki idan kungiyar ta yi watsi shirin ficewar da gwamnatin ta London ta gabatar mata.

Bayan zuwansa kan karagar mulki a karshen watan yulin da ya gabata, tare da alkawalin ganin ko ta halin ya ya sai ya bambare Britaniya daga cikin hadakar kasashen turai, shugaban gwanatin mai tsatsauran ra’ayi ya bayyana aniyar gabatar da shawarwarinsa a birnin Brudelles, shawarwarin da ya ce na gaskiya da amfani ga kasashen na turai.

Mr Jonson dake jawabi a wajen taron shekara shekara na jam’iyarsa ta masa tsatsauran ra’ayi a Manchester arewa maso yammacin kasar Ingla, Ya ce Britaniya na da hanyoyin samun mafita don haka yana tsammanin abukansu na turai za su fahimci haka, suma a samu mafita daga nasu bagaren

Sabanin haka kuma pm na Brtaniya bai shiga raba daya biyu ba, ya yi barazanar cewa, matsawar aka yi watsi da shawarwarin da kasarsa za ta gabatar a ranar 31 ga wannan wata na satumba da muke ciki tokuwa babu makawa kasar ta britaniya zatashura takalmanta ta fice ba tare da yarjejeniya ba, al’amarin da zai iya zama mummunan koma bayan ga kasuwar hanayen jari ta birnin Landon

Manufar wannan sabon ta yi dai shi ne, domin kaucewa ficewar bagatatan, da za ta iya jawo cecekuce kan iyakar yankin Irland, a karin da ake na kawo karshen wannan jerangangiya da aka share tsawon shekaru 3 da ta jefa Brtaniya a cikin makeken rikicin siyasa mai girma

Exit mobile version