Tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Ingila ta yi nasarar lashe kofin matasa na ’yan ƙasa da shekara 17, bayan da ta casa Spaniya da ci 5-2.
Ƙasar Spaniya ce ta fara cin ƙwallo biyu ta hannun ɗan wasan Barcelona Sergio Gomez, sai daki kafin a tafi hutun rabin lokaci Ingila ta zare ƙwallo ɗaya ta hannun Rhian Brewster kuma ƙwallonsa ta takwas da ya ci a gasar.
Ingila ta samu ƙwarin gwiwar farke ƙwallonta ta biyu ta hannun Morgan Gibbs white inda wasan ya koma 2-2. Ingila ta ƙara cin kwallo biyu ta hannun yan wasanta Phil Fodaen wanda yaci ƙwallo ta uku sannan sai Marc Guehi ya ci na biyar.
A kwanakin baya ma tawagar yan wasan ƙwallon ƙafar ƙasar Ingila ce ta lashe kofin duniya na matasa ‘yan ƙasa da shekara 20 da aka yi a watan Yuni.
Brazil wacce ta yi rashin nasara a hannun tawagar yan wasan ƙasar Ingila a wasan daf dana karshe, sai dai ta doke Mali ne ta hannun Alan fortuitous da kuma Yuri Alberto a fafatawar da suka yi a Kolkata a ranar Asabar a wasan neman na ukun.
Mali wacce ta yi rashin nasara a wasan daf da ƙarshe a hannun ƙasar Spaniya ta zama ta hudu a gasar ta matasa ta duniya, duk da cewar ita ce zakara a nahiyar Afirka.