Abba Ibrahim Wada" />

Ingila Ta Raina Mu Kafin Karawarmu, In Ji Modric

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dan kasar Crotia ya bayyana cewa kafin su fitar da kasar Ingila daga gasar cin kofin duniya ‘yan kasar sun rainasu sosai saboda basu da manyan ‘yan kwallo.
Kasar Croatia ta samu nasarar tsallakawa zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Rasha bayan ta doke Ingila da kwallaye 2-1.
Yanzu haka Croatia wadda a karon farko kenan da take samun gurbi a wannan mataki, za ta kece raini da Faransa a wasan karshe a ranar Lahadi.
Kasashen biyu sun fara shafe tsawon mintina 90 suna kan kunnen doki 1-1, lamarin da ya sa aka kara musu lokaci, yayin da Croatia ta kara kwallo ta biyu ta hannun Mario Mandzukic.
Ingila ce ta fara zura kwallo a minti na 5 da saka wasan ta hannun Kieran Trippier, amma Iban Perisic ya farke a minti na 68.
Tarihi ya nuna cewa, a can baya, kasashen biyu sun hadu sau daya a wata babbar gasa, in da Ingila ta samu nasara da ci 4-2 a matakin rukuni a shekarar 2004 a gasar cin kofin kasashen Turai.
Amma a jumulce, sun hadu sau takwas, in da Ingila ta samu nasara a wasanni hudu ,Croatia ta samu nasara a wasanni uku, sannan suka tashi canjarasa a wasa guda daya.

Exit mobile version