Ingila Tana Fatan Karya Mummunan Tarihin Shekara 55 A Gobe

Ingila

Tawagar ‘yan wasan kasar Ingila tana fatan karya tarihin shekara 55 ba tare da lashe wata babbar gasa ba a duniya a ya yinda take shirye shiryen buga wasan karshe da tawagar kasar Italy a gobe Lahadi.

Dan wasa Harry Kane ne ya zura kwallon karshe a kurarren lokaci bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron raga ya bai wa Ingila nasarar lallasa Denmark da kwallo 2 da 1, wanda ke nuna tawagar ta samu sukunin kai wa wasan karshe karon farko cikin shekaru 55, inda za ta kara da Italiya wadda ta fitar da Spain a wasansu na ranar Talata.

Tun a minti na 30 Denmark ta zura kwallonta ta farko ta hannun dan wasanta Mikkel Damsgaard ko da ya ake ingilar ta farke tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci amma fa ta hanyar kuskuren kwallon da Simon Kjaer ya zurawa kasarsa da kansa, gabanin samun bugun fenaritin da Harry Kane ya zura kwallo a mintin karshe.

Wasan wanda ya gudana a filin wasa na Wembley da ke London gaban ‘yan kallo kusan dubu 60 magoya baya sun barke da sowa tare da rungumar juna ba tare da tunanin matakan hana yaduwar cutar corona ba, saboda murnar kaiwa matakin wanda rabon Ingila da shi tun kafin a haifi kowanne daga cikin ‘yan wasan na ta har ma da shi kansa kocin Gareth Southgate mai shekaru 50.

Ba kadai wadanda ke cikin filin na Wembley ba daren na Laraba ya zama gagarumin biki ga iyalai da dama a kasar inda inda aka kwana ana shagugulan nasarar wasa wanda da yawa basu taba ganin irin wannan nasarar ba.

Tsohon dan wasan gaba na Ingila da ke cikin tawagar da doka gasar cin kofin Duniya ta 1966 da Ingilar ta yi nasara kan Jamus Gary Lineker ya ce bai yi tunanin yana da dacen sake ganin kasarsa a wasan karshe karkashin wata babbar gasa ta Duniya ba.

Me masu Koyarwar Suke Cewa?

Kociyan tawagar kasar Ingila, Gareth Southgate, ya bayyana cewa lokaci ya yi da tawagar ‘yan wasan kasar za ta kafa tarihin lashe gasar cin kofin nahiyar turai bayan samun damar zuwa wasan karshe a ranar Laraba.

“Mun shirya kafa tarihin da aka dade ana jiran wadanda zasu kafa shi a duniya kuma ina fatan duk wanda yake da soyayyar Ingila a zuciyarsa ya yi kokarin ganin ya taimaka wajen lashe wannan kofi” in ji Southgate

Ingila ta kai wasan karshe a gasar nahiyar Turai ta Euro 2020, bayan da ta doke kasar Denmark da ci 2-1 bayan da Denmark din ta fara zura kwallo a raga ta hannun Mikkel Damsgaard sauran minti 15 a je hutun rabi lokaci a wasan da suka buga a filin wasa na Wembley dake birnin London.

Kawo yanzu kwallo daya ce kacal ta shiga ragar Ingila tun da aka fara gasar Euro 2020 ta bana daga watan Yunin daya gabata kuma da wannan sakamakon Ingila za ta buga wasan karshe da Italiya ranar Lahadi a dai filin wasan na Wembley.

Tawagar kasar Italiya ta kai wasan karshe ne tun a ranar Talata, bayan da ta yi nasara a kan kasar Sifaniya da ci 4-2 a bugun fenariti, bayan da suka tashi 1-1 kuma kociyan Ingila yace sun shirya kafa tarihi.

Mun Shirya Tunkarar Ingila – Roberto Mancini

Shima mai koyar da tawagar kwallon kafar Italiya, Roberto Mancini ya ce shakka babu sun sha wahala matuka kafin samun nasarar doke tawagar ‘yan wasan kasar Spain domin kaiwa zagayen wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar turai da a yanzu haka ake bugawa kuma yana fatan samun nasara a wasan karshe da Ingila.

Shi ma fitaccen dan wasan kasar ta Italiya Leonardo Bonucci ya bi sawun kocin nasu wajen bayyana wahalar da suka sha a wasan na ranar Talata inda ya ce sunyi iya yinsu domin ganin sun samu wannan nasara kuma sun shirya doke Ingila.

Bonucci ya kara da cewa wasansu da Spain shi ne wasa mafi wahala da ya buga a tsawon lokacin da ya shafe yana haskawa a kwallon kafa kuma yana fatan wasan karshen da za su kece raini da Ingila zaizo musu da sauki sosai.

Exit mobile version