Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Birni da Kewaye, Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, inda ya ce rikicin cikin gida na tsananta a jam’iyyar.
Cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan ranar 11 ga watan Nuwamban, 2025, da ya aike wa Shugaban Jam’iyyar na mazaɓar Zaitawa, da ke Ƙaramar Hukumar Kano Birni.
- Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa
- Sin: Amurka Ba Ta Sa Lura Ga Kare Hakkin Dan Adam
Koki ya ce ya yanke wannan hukunci ne bisa ‘yancin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi na ‘yancin kasancewa a ƙungiya, kamar yadda Sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada, tare da tanade-tanaden Sashe na 7.1 na Kundin Tsarin jam’iyyar NNPP da sauran dokoki masu alaƙa da hakan.
A cewar Koki, rikicin shugabanci a matakin jam’iyyar na ƙasa ne ya sa abin ya zama abu mai wahala a gare shi na ci gaba da zama tare da gudanar da aikinsa yadda ya kamata da kuma samar da ingantaccen wakilci ga jama’arsa a Majalisar Wakilai.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Koki bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba, ko inda ya nufa a siyasance nan gaba.














