Connect with us

WASANNI

Inter Milan Ta Shirya Sayen Messi, In Ji Marotta

Published

on

Shugaban kungiyar kwallon kafar Inter Milan, Giuseppe Marotta ya bayyana aniyar sayan fitaccen dan wasan gaba na kungiyar     kwallon kafa ta Barcelona Lionel Messi, wanda ake ganin karshen zamansa a kungiyar ta kasar Sipaniya yazo karshe.
Giuseppe Marotta ya bayyana sayen dan wasa kamar Lionel Messi abu ne da kowa ke bukata sai dai wanda ya rasa, ya yin da yake maida martani dangane da rade radin komawar dan wasan zuwa kungiyar ta gasar Serie A.
Sai dai shugaban na Inter Milan ya yi watsi da jita-jitar, da ke cewa “babu wata kungiyar Italiya da ta isa sayen Messi inda yace indai kudi zai iya sayan dan wasa babu dan wasan da zai gagari wata kungiya a kasar Italiya a duniya.
“Messi babban dan wasa ne kuma kowacce kungiya zata so ace yana buga mata wasa kamar yadda muma muke fata saboda haka idan har Barcelona tana niyyar rabuwa dashi a shirye muke da mu biya abinda ake bukata” in ji Marotta
Ya ci gaba da cewa “Idan har akwai kungiyoyin da za su iya sayan Messi a duniya a wasu kasashe to a kasar Italiya ma za’a samu saboda akwai kungiyoyi masu karfin tattalin arziki a kasar sannan kuma Messi ko nawa aka saye shi ba za’ayi dana sani ba saboda babban dan wasa ne a duniya har ila yau yana da kwarjini da kima a idon duniya a harkar kwallo”
Messi mai kyautar Ballon D’or har guda 6 a tarihi, ya shiga shekara ta karshe na kwantaraginsa da Barcelona, kuma da alama ya fara gajiya da kamun ludayin kungiyar da ya kwashe tsawon rayuwarsa.
Advertisement

labarai