Inuwar Matan Tijjaniyya Faira Ta Yi Kokari –Sayyada Ummuhani

Sayyada Ummuhani diya kuma fitacciya daga cikin ‘ya’yan Shehu Ibrahim Inyass ta Bayyana cewa taron da kungiyar Inuwar Matan Tijjaniya Faira ta shirya a karo na farko wannan ba karamin kokari bane don haka abin farin ciki ne da karfafa kwiwa ga al’ummar musulmi musamman mabiya darikar Tijjaniya Faira.
Sayyada Ummuhani Shehu Ibrahim Inyass ta bayyana haka ne a lokacin taron kungiyar inuwar matan tijjaniya wacce ke karkashin Malama Fatima Muhammad Tahir a lokacin da take gabatar da jawabi a matsayin Sayyada Ummuhani na babbar bakuwa a wannan taro na matan Tijjaniyya Kano ta kuma bayyana cewa koyarwar Shehu duk musulmi mai kalmar Shahada Dan Uwan Musulmi ne.
Ita shugabar kungiyar Malama Fatima Muhammad Tahir ta bayyana cewa wannan kungiya an kafa ta ne yau kimanin shekara guda da ta wuce kuma makasudin kafa wannan kungiya shi ne wayar da kan mabiya wannan darika hakikanin ilimin sufanci da kuma falala da albarkar da take cikin wannan darika ta Tijjaniyya, haka kuma wannan kungiya na taka muhimmiyar wajen tallafawa marayu ta fuskar abinci, sutura, ilimi da dai sauran abubuwa na jinkai ga mabukata a cewar shugabar kungiyar matan Tijjaniyya Faira ta Kano.
Ita kuwa Sayyada Zainab Shaikh Musa Kallah wacce ta yi dogon bayani mai ratsa jiki ta nesanta darikar Tijjaniyya da ‘yan hakika masu halatta komai da sunan wai su ‘yan Tijjaniyya ne don haka ta yi kira ga shehunan malaman Tijjaniyya da su dukufa wajen bayyana ilimi tun daga tushiyarsa musamman a wuraren manyan tarurruka da mabiya darika ke yi a lokuta daban daban, kamar yadda malaman darikar na baya su ka yi, ta ce sau da yawa a kan gabatar da jawabi ne daga kan ganye da reshe maimakon daukowa tun daga tushe har zuwa reshe da ganye domin gane falal da madadi da ke cikin wannan darika ta Tijjaniyya. Shi kuwa Dr. Tahir Adamu Baba Impossible uban kungiyar bayyana gudummawa da kuma sadaukarwar da Shehu Ibrahim Inyass ya yi wa addini a duniya bakidaya.

Exit mobile version