Hankalin Jama’a da dama na daukuwa ga kudirin nan na rage yawan shekarun tsayawa takara ga Matasa na daga shekaru 30 zuwa 25 a Majalisar Tarayya da kuma Majalisar Dattawa daga 35 zuwa 30 har ma da Gwamnoni da kuma batun dan takara mai zaman kansa ba tare da Jam’iyya ba.
Kudirin ya samu karbuwa sosai inda yanzu kawai ake jiran ganin jihohi 23 sun amince da shi sannan ya zama doka a share fili a bar mai doki da zamiya!
Sau da yawa Matasa na korafin cewa su ne za su magance matsalolinsu da kansu, kuma su ne ke da jini a jika da ya kamata su shugabanci al’umma kamar kuma yadda su ne da ruwa da tsaki a cikin lamurran siyasa tun daga sanya koko ko madara a lika fastoci.
A lura da kyau ba hawan kuka ba ne matsala, a hawo sulbi ya sanya a sulalo kasa tun ba a dade ba, musamman ma idan ba tumbuke takalmi ba. A irin wannan siyasar ta kasar nan akwai tarnaki mai yawa musamman ma ta fuskar kudaden takara da batun an saba da Jam’iyyu da kuma matsalar rashin cikakken hadin kan Matasa.
Babu kuma wanda ba zai sanyo hakan ba abin misali da jin dadi, amma ko Matasan za su iya yin takarar?
Wannan ita ce tambayar da ba haka nan kawai ya kamata a amsa ta ba sai an nazarci amsoshin da za a iya badawar.
A fara kallon Jam’iyyar matasan da ma irin goyon bayan da take da shi,ko Matasan suna wayar da kan ’yan uwansu ta hanyar yin gangami da kuma tsayuwa da kafafunsu?Ko matasan na da nauyin Aljihun yin watanda da kudi a siyasar kasar nan kamar yadda aka saba?
Ko suna da Matsan da iyayen gidansu ne da za su tsaya masu a yayin da duk wani kalubale ya taso masu?Sannan da wadanne alkawurra ne ake tafiya a kansu ga Matasan da har za a gamsar da su cewa Matasa ne kadai Mafita a 2019?
Ko naya ga wadannan lamurran da suke zama kandagaren bakin tulu,sai kuma a kalli batun yadda za a amshi mulki daga wadanda ke sama kuma ba Matasa ba masu kudin da suka raba kan matasan domin cin gashin kansu,kuma su biya matasa don yin ta’asa da goya masu baya kan manufofinsu.
Su ne fa Kungiyoyin Matasa dalibai,da na yankunan Kasar nan da masu fafutukar suna neman ci gaba ne suke ta faman yi wa maula a Abuja da garuruwansu a jihohinsu.
Kuma ga mamaki su ne yawanci da ba su da wani cikakken tsari na taimakon Matasa da suka shata ko suke bi don inganta rayuwar Matasan.
Kowane Matashi yana da ruwa da tsaki kan lamurran da suka jibanci ’yan uwansa. Babu ko shakka nasararmu duka ta kowa ce don Matasan ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, to amma har yanzu amsar tambayar za a ci gaba da nemanta ta cewa Shun ko Matasa na Iya Yin Takara?
Tare da
Kabir Sa’idu Bahaushe
kibdau:kabeerlokuacious77@gmail.com