Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
’Yan kabilar Igbo mazauna Jihar Bauchi sun bukaci a yi watsi da kudirin tsirarun masu fafatukar kafa yankin Biyafara (IPOB), a cewarsu Nijeriya kasa ce wacce kundin tsarinta bai amince da irin wannan manufa da abubuwan da tsiraru masu fafatukan ke tafiya a kai ba. mazaunan sun ce sam su basu goyon bayan wannan shirin da kuma yunkurin na su Nnamdi Kanu da tawagarsa ke tafiya akai.
Shuwagabanin ’yan Kabilar Ibo mazauna Bauchi da suka hada da Rabaran Dominic Nkwocha shugabansu, hade da rakiyar Sakataren kungiyar Janar Patrick Onuorah hade da kuma wasu jiga-jigai da shuwagabanin ‘yan kabilar ne suka bayyana hakan a ganawarsu da manema labarai a Sakatariyar ’yan jarida da ke Bauchi a ranar Asabar 16 ga watan Satumbar 2017.
Shugabannin sun ce ’yan kabilarsu suna nan akan matsayarsu da kuma abubuwan da aka tattaunawa aka kuma tsaya a kai da kungiyar gwamnoni a kwanakin baya.
Hakazalika tawagar ’yan kabilar na Ibo sun nanata cewa za su ci gaba da mutunta doka da kuma oda, kana za su kasance masu ci gaba da yi wa dokokin kasa biyayya da kuma mutunta zamantakewar al’umma musamman a yankunan da su ke “Muna jinjinawa gwamnatin jihar Bauchi a bisa yadda take kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ciki da wajen jihar, domin jin dadn al’umma mazauna jihar. Don haka muna kira ga gwamnati da ta ci gaba da wannan kokarin nata”. In ji su
Shugaban Ibo mazauna Bauchi Rbaran Dominic Nkwocha ya shawarci jama’ansu da suke zaune a jihohin arewa maso gabas da su ci gaba da kwantar da hankali, domin gwamnonin jihohin da jami’an tsaron yankunan sun yi musu alkawarin kare lafiyarsu da dokiyoyinsu. Don haka su ci gaba da mutunta dokokin kasa da biyayya ga dokar Nijeriya a kowane lokaci.