IPOB Ga Buhari: Ka Manta Da Takarar 2019

Daga Umar A Hunkuyi

 

Kungiyar tsagerun Biafra, wacce aka fi sani da IPOB, ta kirayi Shugaba Muhammadu Buhari, da ya manta da kwadayinsa na sake yin takarar shugabancin kasarnan a babban zaben 2019, ko kuma ta tona masa asiri.

Kungiyar tsagerun kuma, ta kirayi wadanda ta kira da, ‘’Yan mafiyan Fulani’ da su jingine tafiyan da Shugaba Buhari, ke shirin yi zuwa Amerika, su kuma ja kunninsa da ka da ya sake ya yi takara a matsayinsa na, Buhari, a 2019.

Cikin wata takardar bayanin da kungiyar tsagerun ta fitar ranar Litinin ta hannun Kakakin ta, Emma Powerful, kungiyar ta ce, samun nasarar kammala abin da ta kira da, ‘Operation Cow Dance,’ da ta yi a kasar Ingila, wanda shi ya sabbaba barowan Shugaba Buharin matsugunin na shi na Ingila ba da shiri ba a ranar Juma’a 20 ga watan Afrilu 2018, ya kuma dawo gida Nijeriya, kungiyar ta ce, hakan ya nu na karfin da take da shi ne.

Sanarwar kungiyar tsagerun ta, IPOB, ta ci gaba da cewa, “Babban kuskuren da, ‘’Yan mafiyan Fulani’ suka yi shi ne, na hana Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya dare kujerar mulkin kasarnan a lokacin da Buharin asalin ya mutu. Shugaban mu, na sane da cewa, gabatar da wannan mutumin mai suna Jibril a madadin Buhari, shi ne ya bayar da cikakkiyar daman rugujewar kasarnan, kan haka ne ma ya hanzarta shelanta cewa, Jibril fa ba Buhari ne ba. shugaban mu ya san tabbatar da cewa, Jibril fa ba Buhari ne ba, shi ne hanya ma fi sauki ta kawo karshen Nijeriya da kuma tabbatuwan kasar Biafra.”

“Kungiyar mu ta ‘yan asalin yankin Biafra, IPOB, ta sha alwashin ci gaba da fafutukarta na bayyana wa duniya ainihin wannan mutum mai suna Jibril, da yake shigan burtu da sunan shi ne Buhari.”

“Kan haka ne muka kuduri aniyar gabatar da, ‘Operation COW DANCE 2,’ bayan samun nasarar na farkon, domin wannan ya dace da zuwan, ‘Muhammadu Buhari,’ birnin Washington, ranar 30 ga watan Afrilu. Babban manufar wannan, ‘Operation COW DANCE 2,’ da za mu kaddamar a kasar ta Amurka, shi ne, domin mu kama mu kuma mika mutumin da yake yin wannan aiki na shigan burtu da sunan Buhari, yake yaudarar milyoyin al’umma a duniyar nan. Domin a yi ma shi gwajin DNA.”

“IPOB, za ta tabbatar wa da duniya cewa, Jibril fa ba Buhari ne ba, Buhari ya mutu tun a farkon shekarar 2017, an kuma rufe shi ne a kasar Saudi Arabiya. Za mu yi duk mai yiwuwa wajen samun DNA din Jibril a wannan tafiyan da yake shirin yi zuwa Amerika.

“Don haka, duk yanda masu kula da shi za su yi a can Amerika din, tilas ne Jibril ya bar samfurin DNA, din shi wanda za mu kwatan ta shi da na daya daga cikin ‘ya’yan Buhari, ko kuma na wata kanwarsa wanda suke a hannun mu yanzun haka.”

 

Exit mobile version